Kotu ta soke zaɓen fidda gwani na gwamna na PDP a Ekiti

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Ado-Ekiti ta soke zaɓen fidda gwani na gwamna da jam’iyyar PDP ta gudanar a jihar Ekiti gabanin zaɓen shekarar 2026.

Kotun ta kuma umarci jam’iyyar da ta sake gudanar da sabon zaɓen fidda gwani bisa bin doka da ƙa’idojin cikin gida na jam’iyyar.

Alƙalin kotun, Babs Kuewumi, ne ya yanke hukuncin a ranar Talata a karar mai lamba FHC/AD/CS/29/2025, wadda Funso Ayeni, dan takarar gwamna, ya shigar kan PDP da Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC).

Ayeni ya kalubalanci sahihancin zaben fidda gwanin da ya fitar da Wole Oluyede, yana mai cewa jam’iyyar ta “gaza gabatar da sahihin jerin sunayen wakilan doka da na wucin gadi” da aka yi amfani da su wajen gudanar da zaben.

Ya ce rashin gabatar da asalin jerin wakilan ya saɓawa ƙa’idojin PDP da kuma Dokar Zaɓe, lamarin da ya sanya zaɓen fidda gwanin ya zama ba shi da inganci.

A cikin hukuncinsa, Kuewumi ya ce yadda aka gudanar da zaɓen fidda gwanin bai yi daidai da tanade-tanaden doka da kundin tsarin jam’iyyar ba.

Saboda haka, alkalin ya soke zaɓen tare da umartar PDP da ta sake gudanar da sabon zaɓen fidda gwani na gwamna cikin  bin doka da ka’idoji. Ya kuma umarci INEC da ta sa ido kan zaɓen.

Har ila yau, ya ce dole ne a bar dukkan ‘yan takara masu cancanta su shiga sabon zaɓen domin tabbatar da gaskiya, adalci da dimokuraɗiyya a cikin jam’iyyar.

By ukarofi