
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, ta ƙaddamar da bincike akan ƙorafin da Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote ya shigar mata akan tsohon shugaban hukumar gudanarwar man fetur ta ƙasa (NMDPRA), Farouk Ahmed inda ya zarge shi da cin mutuncin aiki da kashe-kashen kuɗaɗen al’umma ta haramtattun hanyoyi.
Bincike jarida NewsPointNigeria ya nuna cewa hukumar ta fara ɗaukar matakan binciken da ya dace da al’amarin ciki har da aike wa cibiyoyin gida da na ƙasashen waje saƙonni akan ƙorafin musamman ga makarantar sakandare ta ƙasar Switzerland da aka ce a nan ‘ya’yan Farouk Ahmed suka yi karatu.
A watan Disambar 2025 Ɗangote ya damƙa wa Hukumar Yaƙi da Manyan Laifuka (ICPC) ƙorafin nasa, inda ya yi zargin cewa Ahmed ya kashe jimillar Dala miliyan 7 a iya kararun ‘ya’yansa a Switzerland yayin da yake shugaban NMDPRA.
A ciki, ya zargi tsohon shugaban na NMDPRA da taka kundin dokar harkokin jami’an gwamnati ta hanyar karkatar da dukiyar ƙasa zuwa ƙasashen waje don karatun ‘ya’yan nasa, lamar da ya ce ya saɓa wa doka da ƙwarewar aiki.
Daga bisani, Ɗangoten ya janye ƙarafin nasa a ranar 5 ga watan Junairu ta lauyansa, wanda duk da haka ICPC ta ci alwashin gudanar da bincike akan al’amarin bisa tsarin doka.
Wani jami’i EFCC da ya nemi a sakaye sunansa, ya ce tuni hukumar ta shiga gudanar da bincike akan al’amarin musamman akan al’amuran da suka shafi ikirarin attajirin ɗan kasuwar akan tsohon shugaban na NMDPRA.
