Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Rundunar ’yan sanda ta jihar Kano ta kama mutane uku da ake zargi da hannu a kisan gillar wata uwa da ’ya’yanta shida da aka yi a unguwar Ɗorayi Chiranchi da ke cikin birnin Kano.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Lahadi.
Kamen ya biyo bayan wani aiki na musamman bisa bayanan sirri, wanda aka gudanar bisa umarnin sufeto janar na ’yan sanda, Kayode Egbetokun, tare da kulawar kwamishinan ’yan sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori.
A cewar rundunar, an kama wadanda ake zargin ne a wani samame da aka gudanar daga ƙarfe 10:00 na dare a ranar 17 ga Janairu zuwa ƙarfe 4:00 na asubahin ranar 18 ga Janairu, 2026.
Waɗanda aka kama sun haɗa da Umar Auwalu, mai shekaru 23 daga unguwar Sabuwar Gandu; Isyaku Yakubu da aka fi sani da “Chebe”, mai shekaru 40 daga unguwar Sagagi; da Yakubu Abdulaziz wanda aka fi kira “Wawo”, mai shekaru 21 daga unguwar Sabon Gida Sharaɗa.
Kazalika, ‘yan sanda sun bayyana cewa wanda ake zargin jagorantar kisan, Umar Auwalu, wanda ɗan uwa ne ga marigayiyar, ya amsa laifin aikata kisan. Haka kuma, ya bayyana cewa sun aikata wasu kashe- kashe masu tada hankali a wasu sassan Kano a baya-bayan nan.
Daga cikin abubuwan da aka ƙwato daga hannun waɗanda ake zargin akwai tufafi masu tabon jini, wayoyin salula biyu na marigayiyar, adda, gora, kuɗi da ake zargin an ƙwace a wajen da abin ya faru, da wasu makamai masu haɗari. Rundunar ta ce bincike na ci gaba.
Daga nan rundunar ’yan sanda ta Jihar Kano ta yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin, tare da gode wa al’umma bisa addu’o’i, goyon baya da haɗin kai. Rundunar ta kuma tabbatar wa jama’a ƙudirinta na ganin an gurfanar da duk masu aikata laifuka a gaban kuliya.

