
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jihar Kano ta shiga halin ɗaukewar wutar lantarki sakamakon yajin aikin da ma’aikatan Kamfanin Raba Wutar Lantarkin jihar (KEDCO) suka shiga, lamarin da ya haifar da tsaiko ga harkokin tattali da lamuran jama’a na yau da kullum a cikin birni da kewaye.
Wannan al’amari ya haddasa gagarumar asara musamman ga ‘yan kasuwa da ke buƙatar lantarki yayin gudanar da kasuwancinsu.
An fara yajijn aikin ne a ranar Laraba ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar manyan jami’an wutar lantarki da kamfanoni masu alaƙa da su (SSAEAC) da ƙungiyar ma’aikatan wutar lantarki (NUEE) biyo bayan ƙarewar wa’adin da suka ba hukumar gudanarwar KEDCO a ranar Talata, 20 ga Junairu, 2026 batare da warware matsalolinsu ba.
Tun a safiyar Laraba ne mambobin ƙungiyoyin suka rufe guraben ayyukansu na KEDCO ciki har da hedikwatar kamfanin da wasu manyan cibiyoyi, lamarin da ya jefa birnin Kano da kewayenta cikin yanayi na duhu.
Wannan mataki ya haddasa cikas ga harkokin kasuwanci, ayyana asibitoci, samar da ruwan amfanin yau da kullum, harkokin sanarwa da sauran al’amuran al’umma na kullum, inda al’amarin ya yi ƙamari yayin da aka shiga kwanaki na uku.
Da yake zantawa da manema labarai jim-kaɗan bayan rufe babban ofishin na KEDCO, Mataimakin Shugaban SSAEAC na Arewa, Rilwan Shehu ya ce tsunduma yajijn aikin ya zama wajibi saboda gazawar hukumar gudanarwar wajen cika alƙawuran yarjejeniyoyin da aka ɗauka tun tsawon lokaci.
Ya bayyana cewa, ƙungiyoyin sun yi haƙuri na tsawon shekaru, inda a yanzu ba su da wani zaɓin da ya wuce tafiya yajin aiki.
