
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya zargi majalisar dattawa da jan ƙafa da gangan akan aikin gyaran dokar zaɓe ta 2022, yana mai gargaɗin hakan ka iya zama barazana ga sahihancin zaɓen 2027.
Atiku, wanda kuma ɗan takarar shugaban ƙasa ne a zaɓen 2023, ya ce rashin gyaran dokar zaɓen ƙasar ne ya janyo kurakuren da aka tafka a zaɓen 2023 a Nijeriya.
Dokar zaɓen ta 2022 da aka sanya wa hannu a watan Fabarairun 2022 ita ce ake amfani da ita wajen gudanar da zaɓuka yanzu haka a Nijeriya.
Yanzu haka wannan doka tana a gaban majalisar dokokin ƙasar, inda ake nazari da muhawara a kai da nufin gyara sassan da aka gano cewa suna da matsala ta la’akari da abubuwan da suka faru a lokacin babban zaɓen Nijeriya na 2023. Kuma wannan wani mataki ne na shirya fuskantar zaɓen 2027 a Nijeriya.
Wani saƙo da tsohon mataimakin shugaban Najeriyan ya wallafa a shafinsa na X ya ce sassan da ke buƙatar gyara a dokar zaɓen ƙasar ta 2022, su ne suke hana masu ƙorafi kan sakamakon zaɓe damar iya kare abubuwan da suke ƙalubalanta a gaban kotu.
Daga cikin sassan da aka shirya gyarawa a dokar zaɓen ta Nijeriya, waɗanda Atiku Abubakar ke fatan su tabbata harda “Tura sakamakon zaɓe ta na’ura mai ƙwaƙwalwa, da kuma batun samar da kotu mai zaman kanta da za ta saurari ƙarar waɗanda suka aikata laifunkan zaɓen” kamar yadda ya bayyana ta kafar X.
Ya ce, a bisa nazarinsu, a bayyane yake cewa majalisar ba ta da aniyar kammala wannan aiki domin inganta tsarin gudanar da zaɓe a Nijeriya, yana mai zargin cewa da gangan majalisar dattawan ke hana a aiwatar da kundin dokar zaɓen.
