Majalisar Wakilai na shirin haramta wa ’yan sanda bayyana waɗanda ake zargi a bainar jama’a

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Majalisar Wakilan Nijeriya na duba ƙudirin gyaran Kundin Tsarin Mulki da zai hana ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro nuna masu laifi da mutanen da suka kama kafin a gurfanar da su gaban kotu.

Wannan mataki ya biyo bayan dogon suka da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam, ɓangaren shari’a da ƙungiyoyin farar hula ke yi kan wannan ɗabi’a tsawon shekaru.

Rahotanni sun nuna cewa ƙudirin ya fito ne daga shawarwarin da Kwamitin Majalisar kan Gyaran Kundin Tsarin Mulki, wanda Mataimakin Kakakin Majalisar, Benjamin Kalu, ke jagoranta, ya amince da su.

Ana sa ran najalisar za ta fara muhawara kan ƙudirin ne bayan dawowarta daga hutun Kirsimeti da sabuwar shekara.

A tsakiyar ƙudirin akwai shirin yin gyara ga Sashe na 34 na Kundin Tsarin Mulkin 1999, wanda ke kare mutunci da martabar ɗan Adam. 

A halin yanzu, sashen ya tanadi cewa kowane mutum yana da ‘yancin a mutunta shi, tare da haramta azaba, wulaƙanci ko wani abu da zai tauye mutuncinsa, haka kuma ya hana bautarwa.

Sabon ƙudirin na neman faɗaɗa ma’anar azaba da wulaƙanci, inda ake shirin ƙara wani sashe da zai bayyana ƙarara cewa nuna mutanen da aka kama a bainar jama’a ma yana cikin azaba da wulaƙanci da Kundin Tsarin Mulki ya haramta. 

Sabon tanadin ya ce, duk wani aiki na nuna mutane da aka kama a fili, ko da ta wace hukumar tsaro ce, za a ɗauke shi a matsayin tauye mutunci.

Shekaru da dama kenan ana yawan ganin jami’an tsaro suna jera mutanen da suka kama a gaban ’yan jarida, suna daukar hotunansu, har ma wasu lokuta ana tilasta musu kwaikwayon laifin da ake zargin sun aikata, duk da cewa bincike bai kammala ba, kuma ba a kai su kotu ba. Wannan ɗabi’a ta jawo koke-koke da dama, inda kotuna suka yanke hukunci cewa hakan karya haƙƙoƙin ɗan Adam ne kuma amfani da iko ba bisa ƙa’ida ba.

Duk da waɗannan hukuncin kotu, jami’an tsaro sun ci gaba da wannan al’ada, abin da ya kara jawo kiraye-kirayen kafa tsauraran dokoki domin kare haƙƙin jama’a.

Yayin da take mayar da martani kan ƙudirin, fitacciyar ’yar fafutukar dimokuraɗiyya kuma wacce ta kafa ƙungiyar Women Arise, Dakta Joe Okei-Odumakin, ta yaba wa Majalisar Wakilai kan wannan mataki. Ta ce hakan zai taimaka wajen daidaita dokokin Nijeriya da ƙa’idojin ƙasa da ƙasa na kare haƙƙin ɗan Adam.

A cewarta, akwai cikakken haramci na azaba da duk wani nau’i na wulaƙanci a dokokin ƙasa da ƙasa, musamman ƙarƙashin dokokin jin ƙai na duniya da na kare haƙƙin ɗan Adam. Ta jaddada cewa waɗannan dokoki sun samo asali ne daga Yarjejeniyar Geneva ta 1949, da ƙa’idojinta na 1977, da kuma Yarjejeniyar Duniya kan Haramta Azaba ta 1984, da sauran muhimman yarjejeniyoyi.

Ta ce, dokokin jin ƙai na duniya da na kare haƙƙin ɗan Adam suna cike juna wajen kafa tsarin shari’a mai ƙarfi da zai hana azaba da wulaƙanci, tare da hukunta duk wanda ya aikata hakan. Saboda haka, ta bayyana cewa Majalisar Wakilai ta yi daidai da gyaran Kundin Tsarin Mulki domin ya dace da kyawawan ɗabi’u na duniya.

By ukarofi