
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Amurka ta sanar da kammala ficewa daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a hukumance, inda ta ce ɗauki matakin ne bisa la’akari da rashin kula da annobar COVID-19 yadda ya dace, rashin gyara da sanya siyasa daga ɓangaren ƙasashen da ke ƙarƙashin hukumar.
Wannan mataki ya fara aiki ne daga 22 ga Janairun 2026 bayan cika sharaɗin sanarwar shekara guda.
Sakataren Harkokin Wajen ƙasar, Marco Rubio da Sakataren Lafiya Robert F. Kennedy Jr. sun ce matakin ya ‘yantar da Amurka daga takunkumin da hukumar ta sanya wa ƙasashen da ke ƙarƙashin nata.
A cewarta, an dakatar da duk tallafin kuɗi da ma’aikatan Amurka da ke aiki da WHO, kuma daga yanzu Amurka za ta mayar da hankali kan hulɗar kiwon lafiya kai-tsaye da ƙasashe abokan hulɗar ta.
Daraktan Janar na WHO, Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya nuna damuwa kan matakin, yana cewa ficewar ba alheri ba ce ga duniya.
An kafa WHO a 1948, kuma Amurka na daga cikin ƙasashen da suka kafa ta.
Shugaba Donald Trump ya daɗe yana sukar hukumar, musamman akan yadda ta tafiyar da al’amuran COVID-19 da kuma batun kuɗaɗen da Amurka ke bayarwa.
Tun tsawon sama da shekara guda Amurka ta dakatar da bai wa hukumar tallafin kuɗi, janye ma’aikata ‘ya’yanta da sauya wasu hulɗoɗinta daga WHO zuwa yi da wasu ƙasashe da ƙungiyoyi.
