Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wata babbar motar tanki da ke ɗauke da dizel ta kife a kan gadar Liverpool da ke yankin Apapa a Jihar Legas, lamarin da ya haddasa zubewar man a kan titin, inda wasu mazauna yankin suka fara kwashe shi ba tare da la’akari da hatsarin da ke tattare da hakan ba.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin, inda mutane suka riƙa taruwa ɗauke da jarkoki da bokiti domin ɗiban dizal ɗin da ya zube daga tankar motar. Duk da haɗarin fashewa ko kamawar wuta, hakan bai hana wasu shiga tsakani ba suna ɗibar ganima.
Hukumar Kula da Zirga-zirga ta Jihar Legas, LASTMA, ta tabbatar da faruwar lamarin ta shafin ɗ, inda ta bayyana cewa an karkatar da ababen hawa zuwa ɗayan ɓangaren gadar domin tabbatar da tsaro da kauce wa wata mummunar hatsari.
Jami’an agaji daga Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Legas, ’yan sandan Nujeriya, da ma’aikatan LASTMA sun garzaya wurin domin daƙile yiwuwar ɓarkewar gobara da kuma tabbatar da tsaron jama’a. Haka kuma, jami’ai daga Hukumar Kula da Hanyoyi ta ƙasa (FRSC), Hukumar Tsaro ta DSS da Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NPA) sun halarci wurin domin bada tallafi.
LASTMA ta ce, an ɗauki waɗannan matakai ne domin hana ɓarkewar wuta, sauke motar daga kan hanya da kuma tabbatar da ci gaban zirga-zirga cikin tsaro.
Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a tabbatar da ko matsalar birki ce ta janyo kifewar motar ba.
A wani bidiyo da LASTMA ta wallafa, an ga jama’a suna taruwa suna ɗibar dizal ɗin da ya zube, inda babu rahoton kamawar wuta a wurin a lokacin.
Daga bisani, hukumar ta sanar da sake buɗe titin da aka rufe bayan jami’an kashe gobara sun shawo kan zubewar man tare da rage haɗarin tashin gobara. LASTMA ta ce zirga-zirga za ta fara inganta a yankin yayin da ake jiran isowar motar ɗaukar tankar da ta kife.
Duk da haka, hukumar ta bayyana cewa ana ci gaba da amfani da tsarin juyar da hanya domin kula da zirga-zirga, inda motsin ababen hawa ke tafiya a hankali sakamakon cunkoso. Jami’an tsaro sun kasance a wurin domin tabbatar da doka da oda tare da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
