Gwamnatin Sakkwato za ta kafa dokar haramta almubazzaranci kafin aure

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Jihar Sakkwato da haɗin-gwiwar Masarautar Sakkwato ta sanar da shirin sake fasali da tsaurara dokokin da suka shafi kashe kuɗaɗe a yayin bukukuwan aure.

Wannan mataki na nufin sauƙaƙa wa matasa hanyoyin yin aure da rage nauyin da iyaye suke ɗauka a halin yanzu yayin hidimar aurarraki.

Rahotanni sun bayyana cewa an cimma wannan matsaya ne domin magance al’adu da ababen da suke haifar da jinkirin aure ga maza da mata da dama a jihar.

Ana fatan sabbin dokokin za su mayar da hankali ne wajen ayyana takamaiman abubuwan da suka zama wajibi a matsayin sadaki da sauran kayan aure tare da haramta almubazzaranci a yayin ƙayyade su.

Hukumomi a jihar sun ce, tsadar kayan ɗaki da sauran hidimomin biki sun sanya aure ya yi tsada ga talaka, wanda hakan ke barazana ga tarbiyyar al’umma a zamantakewar yau da kullum.

Haka kuma, ana sa ran sabon tsarin zai haɗa da sanya ido sosai ta yadda za a hukunta dukkan wanda ya karya ƙa’idojin da aka gindaya a sassan jihar musamman a yankunan karkara da birane.

Masu sharhi sun yaba da wannan yunƙuri, inda suka bayyana cewa idan har aka aiwatar da dokar yadda ta dace, to za a samu raguwar mace-macen aure da kuma sauƙaƙa wa ma’aurata rayuwa bayan biki.

Kazalika, gwamnatin kuma yi kira ga sarakunan gargajiya da malaman addini da su taya ta wajen wayar da kan jama’a domin karɓar wannan sabon tsarin yadda ake buƙata.

By Babaji