Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Kakakin majalisar dokokin jihar Katsina Rt Hon Nasiru Yahaya Daura ya faɗi haka a taron gangamin da jam’iyar APC na ƙaramar hukumar Daura ta shirya.
Ya ce duba da ayyukan da gwamna Raɗɗa ya aiwatar a faɗin jihar yasa al’ummar ƙaramar hukumar Daura suka shirya waɗannan taron jaddada goyon bayan sake takarar gwamnan.
Kakakin majalisar ya bayyana cewa ɗaukacin al’ummar ƙaramar hukumar Daura da suka haɗa da matasa, ‘yan kasuwa,maza da mata sun shaida cewa gwamna Dikko Raɗɗa zasu yi a 2027.
“Bamu da wani Ɗan takarar sai Dikko Raɗɗa,bamu da wata jami’ya sai APC a ƙaramar hukumar Daura,”Inji Rt Hon Nasiru Yahaya Daura.
Shima shugaban jam’iyar APC a jihar Katsina Sani Aliyu Ahmed a jawabinsa ya ce a duk waɗannan babu wata ƙaramar hukumar da ta amfani da abubuwan more rayuwa kamar ƙaramar hukumar Daura.
Shugaban jam’iyar wanda ɗan asalin Daura ne ya ce al’ummar Daura sun ce da irin wannan abubuwan alheri da Dikko Raɗɗa yayi masu suke jaddada goyon bayan su ga takarar shugaban ƙasa Bola Tinubu da gwamnan Katsina Malam Dikko Raɗɗa a zaɓen 2027.
Ita ma a saƙon ta wajan taron Uwargidan tsohon shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari,A’isha Buhari ta ce ita da iyalin mai gidan ta marigayi sun nuna cikakken goyon bayan su ga takarar gwamna Dikko Raɗɗa.
Ta kuma godewa Gwamnan bisa ɗawainiyar da ya yi a lokacin rasuwarsa mijinta marigayi Muhammadu Buhari.
Mutane naganin wannan taro ba zai rasa nasaba da fitowar tsohon shugaban hukumar tsaro na DSS Alhaji Lawal Musa Daura takarar kujerar gwamnan a ƙarƙashin jam’iyar adawa ta ADC.
