
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar Kano kuma ɗan Sanata Rabiʼu Musa Kwankwaso Rabiu Kwankwaso, wato Mustapha Rabi’u Kwankwaso, ya ajiye muƙaminsa na kwamishina.
Ya bayyana haka ne a wata takardar murabus da Mustapha Kwankwaso ya fitar a ranar Litinin, 26 ga Janairun 2026.
A sanarwar, ya miƙa godiya ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf bisa damar da ya ba shi na yi wa al’ummar jihar hidima a lokacin da yake riƙe da muƙamin.
Ɗan tsohon gwamnan ya kuma yi fatan harkokin matasa da wasanni a jihar Kano za su cigaba da samun kulawa tare da yi wa gwamnati da al’ummar jihar fatan alheri.
Wannan dai na zuwa ne yayin da aka raba gari tsakanin mahaifin nasa da Abba Kabir Yusuf a siyasance.
Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso kwamishinan matasa da wasanni ne jihar a Kano ƙarƙashin gwamnatin Abba Kabir Yusuf.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan ke komawa jam’iyyar APC a wani yanayi na sabon babin siyasar Kano.
