Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Katsina, DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya bayyana haka a wata takardar sanar wa.
Ya ce ofishin ‘yan sanda na garin Dutsi a ƙaramar hukumar Dutsi suka sami bayanan sirri gama da fasa wani ɗakin kayan gwaje-gwaje a wata makarantar sakandare da ke yankin.
Ko da ‘yan sanda suka isa wajen sun tarar da an ɓalle ɗakin kayan tare da sace na’ura mai samar da wutar lantarki (solar) da wasu kayayyaki amma an bar safan hannu.
DSP Abubakar Sadiq ya cigaba da cewa bincike da yan sanda sukayi shine ya kai su ga gidan shugaban makarantar mai suna Musa Bashir ɗan shekara 58 da haihuwa inda suka gano wasu kayan da ake zargin an sace.
Kayan da ‘yan sanda suka gano gidan shi principal sun haɗa da kwanon da ke samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana (solar),Batirorin solar,CPU,Mashin na fitar da takarda (Printing machine)da sauran wasu na’urorin da yan makarantar ke koyon darussa da su.
Jami’in hulɗa da jama’a DSP Sadiq ya tabbatar da kama shugaban makarantar wanda ya amsa cewa shine ya aikata laifin.
DSP Sadiq ya bayyana cewa ‘yan sanda za su cigaba da bincike domin gano sauran kayan da suka ɓace.
