
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Jihar Kano ta yi watsi da ikirarin da aka jingina wa ɗaya daga cikin manyan ƙasa, Injiniya Buba Galadima, cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ba zai iya koma wa mulki ba a karo na biyu sai da taimakon Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, tana mai bayyana hakan a matsayin abin ruɗarwa da rashin sanin tarihin siyasar jihar.
A wata sanrwa da ta aike wa manema labarai a Abuja ranar Lahadi, Kwamishinan Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Waiya, ya ce kalaman sun rage ƙarfin faɗa-a-ji a siyasance na al’ummar Kano da kuma mayar da jihar wadda ke dogara da ubangidancia siyasa.
Ya ce, duk da cewa Kwankwaso ginshiƙi ne a harkokin siyasar Kano, hakan ba dalilin ba ne na mayar da shi madogara a siyasar jihar.
Kwamared Waiya ya kuma bayyana mamakinsa akan yadda kalaman suka fito daga Injiniya Galadima wanda ya amfana da shugabancin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ba shi muƙamin shugaban majalisar jagoranci makarantar Polytechnic ta Kano duk da cewa shi ba ɗan Kano ba ne.
A cewarsa, bisa ga nazarin riƙon muƙamin da Galadima ya yi, babu wani ci-gaba ko sauyi da ya kawo har ya bar kujerar.
Kwamishinan ya ƙara da cewa, ana mu’amalantar shugabanci ne bisa ga sakamako ba cece-kucen jama’a ba, yana mai cewa masu zaɓe a Kano suna da tarihin juya al’amuran siyasarsu.
