Imam Abdullahi Abubakar: Daga mai sha’awar shiga soja zuwa jarumin ceton al’umma

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Ranar 15 ga watan Janairu na kowacce shekara na kasancewa Ranar Tunawa Da Mazan Jiya a Nijeriya, domin yabawa da gudummawar da dakarun sojojin ƙasar nan suka bayar a fagagen fama daban-daban. Wannan rana harwayau ta kasance baƙar rana da al’ummar Jihar Filato, wacce ba za su taɓa mantawa da ita ba, kasancewar ita ce ranar da fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na ƙauyen Yelwan Gindin Akwati, a yankin Nghar da ke ƙaramar Hukumar Barikin Ladi ya yi bankwana da duniya.

Malam Abdullahi ya rasu ne a Asibitin ƙwararru na Jihar Filato bayan ya yi fama da lalurar sarƙewar numfashi, jinyar da bai wuce mako guda yana yi a asibiti ba, amma kuma ya jima yana lallaɓa ta, saboda a cewar makusantansa, ba mutum ne mai son kwanciyar asibiti ba. Ya rasu a ranar Alhamis da daddare, da misalin ƙarfe goma, kamar yadda iyalinsa suka sanar. Har lokacin rasuwarsa Malam bai daina yi wa jama’a nasihar a zauna lafiya ba, babban burin da ya rayu da shi a ransa, kuma da shi ya bar duniya.

Shekaru fiye da hamsin da suka gabata, a cewar ɗaya daga cikin iyalin Malam, lokacin yana matashi bayan ya samu haddar Alƙur’ani daga Maiduguri inda mahaifinsa Malam Abubakar Tsoho ya tura shi, ya dawo gida Yelwa, sai ya bayyanawa babansa buƙatar sa ta shiga soja, domin ya shiga ayarin sojojin gwamnatin Nijeriya a lokacin yaƙin basasar da aka yi da ’yan awaren Biyafira. Amma sai mahaifinsa ya ƙi amince masa, a maimakon haka sai kawai aka yi masa aure, aka tura shi gona.

Ashe wannan jarumta ta Imam Abdullahi ba daga baya ya sameta ba, ya daɗe yana da kishin ganin ya sadaukar da rayuwarsa don ceton ƙasar sa da al’ummarsa. Kamar yadda muka gani ya nuna a lokacin harin ta’addanci na 2018. Kodayake mutane ƙalilan ne suka san da wannan tsohon buri na Malam, amma da dama daga waɗanda suka zauna tare da shi sun zan shi jajirtacce ne, ƙaƙƙarfa, kuma marar tsoro.

Abin mamaki, sai ga shi Imam ya rasu a ranar tunawa da mazan jiya, waɗanda suka sadaukar da rayukansu a yaƙin basasa da sauran yaƙe-yaƙen da sojojin Nijeriya suka shiga. Bai shiga soja ba, amma ya ba da rayuwarsa da irin jarumta ta sojoji don ceton rayukan al’ummar sa.

Rayuwar Imam cike take da darussa da za mu iya ɗauka mu yi aiki da su a rayuwar mu. Kasancewarsa mutum mai sauƙin kai da rashin ɗaukar kansa a matsayin wani abu, kyakkyawar mu’amalarsa da mutane ta sa ko da bai taɓa haɗuwa da kai ba, da zarar kun haɗu zai tarbe ka da sakin fuska da kyakkyawar magana. Yana da sanyin hali da sanyin magana. A duk haɗuwar da muka yi da shi, kwarjininsa da fara’arsa tana sa mu rabu zuciyata na shauƙin sake haɗuwa da shi.

A tattaunawa ta da shi ta farko a 2019 shekara guda bayan aukuwar mummunan al’amari da ya faru na rikice-rikicen ƙabilanci a yankin Riyom da Barikin Ladi tsakanin manoma da makiyaya, wanda ya kai ga ya jagoranci babban aikin ceton rayukan daruruwan mutane da suka garzaya wajensa don neman mafaka yayin da ’yan ta’adda suka far wa ƙauyensu, ranar 23 ga watan Yuni na shekarar 2018. Na tambaye shi abin da ya bashi ƙwarin gwiwar nuna wannan sadaukantaka alhalin ko shi ma maharan ba su bar shi ba, don sun hallaka ɗan uwansa a ranar. Amsar da ya bani mai sauƙi ce, ‘Na yi abin da addinin Musulunci ya koyar da ni ne. Wannan ita ce rayuwar da Manzon Allah SAW ya koyawa sahabbansa.’

Malam ya yi abin da ya kamata ne a lokacin da ya kamata, a matsayinsa na jagoran al’umma, kuma mai faɗa a ji. Shi malami ne kawai, ba sarki ko dagaci ko mai anguwa ba. Sana’arsa ba ta wuce karantarwa ba, sai noma da aikin kuza, sana’ar da akasari jama’ar yankin suka fi dogaro da ita. Kasancewar Ubangiji Allah Ya albarkaci wannan ƙasa ta su da arziƙin ma’adanin kuza, wanda daga ita ne jama’ar yankin ke samun arziƙin su.

Sai dai ga duk wanda ya taɓa shiga wannan yanki na su zai fahimci yadda gwamnati ta kawar da kanta daga gare su, duk kuwa da arziƙin da ake fitarwa daga yankin. Babu hanya mai kyau da za a shiga da abin hawa, babu caji ofis ɗin ’yan sanda, ko na ’yan banga. Sai dai shingayen binciken ababen hawa na sojoji da za ka wuce su jifa-jifa a hanya. Amma idan ka shiga cikin ƙauyukan za ka tarar da su suna zaune ne kara zube, ihunka banza, wanda ko da wani abu ya faru a yankin kafin jami’an tsaro su kai musu ɗauki, har an ci su da yaƙi an wuce. Ga shi yankin na fama da matsalar sabis ɗin waya, sai ka fita bayan gari ka hau kan tudu kafin ka samu damar yin waya, ko kuma ka yi ta gwada wasu layukan daban-daban. 

Wannan na daga cikin abin da Imam Abdullahi ya yi ta roƙon gwamnati akai, bai nemi a bashi kuɗi ko wata martaba ba, amma a duba al’ummar sa, a gyara musu hanya, a kai musu jami’an tsaro. A samar musu da makaranta, don ilimin ‘ya’yansu, a kuma kyautata zamantakewar da suke ciki. Wani surukin sa da muka zanta da shi, wanda ake kira da Dakta Isiyaku Yelwa ya bayyana cewa, Malam ya kokawa tsohon shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari game da halin da yankin ke ciki, wanda kuma ya janyo hankalin Gwamnan jihar na lokacin, Simon Lalong, shi kuma ya yi alƙawarin za a duba batun, amma har suka bar mulki babu abin da aka yi.

Kodayake, Imam ya samu shaidar karramawa ta ƙasa daga tsohon Shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari da Gwamnatin ƙasar Amurka a shekarar 2019, da wasu ƙungiyoyi na duniya da suka riƙa karrama shi suna yabawa jarumta da tausayawa rayukan ɗan adam da ya yi. Amma akasari karramawa ce ta takarda, ko kwalin shaida, ko na gilashi mai tsada, da sauran ire-irensu, babu wani tallafi da zai inganta rayuwarsa ko ta jama’ar yankin. 

Za ka yi matuƙar mamaki, idan ka shiga ƙauyen ka ga yadda Malam yake rayuwa shi da iyalinsa, cikin rayuwar talauci da rashin samun kulawa. Kodayake Malam jajirtaccen manomi ne, ba a rasa abin da za a ci a gidansa har ma a bai wa wasu. Amma yanayin rayuwar da ya yi tare da iyalinsa abar tausayi ce. Ba za ka ce shi ne fitaccen malamin nan da duniya ke magana akai ba. Kodayake an ce gwamnati ta taɓa bashi kyautar Naira Miliyan ɗaya, kuma an kai shi ƙasa mai tsarki ya sauke farali har sau biyu, amma ƙaramin ɗansa Saleh Abdullahi ya ce tun kafin Malam ya koma gida daga Abuja ya gama rabar da wannan kuɗin a tsakanin ’yan uwa da abokan arziƙi da ake rayuwa tare.

Imam Abdullahi mutum ne mai tsananin gudun duniya da ƙanƙan da kai. Ba shi da kwaɗayi ko neman suna, da zubar da mutuncinsa a gaban ’yan siyasa. Ya haƙura da inda Allah ya ajiye shi, yana zaune a ƙauyensu cikin iyalansa da jama’ar sa, sai idan an nemi a gana da shi a cikin Jos ko Barikin Ladi, ko kuma wata hidima ta addini, da ta zumunci.

Da yake tunawa da bajintar da Imam ya nuna a lokacin harin 2018, wani shugaban al’umma a yankin, Irmiya Magit ya bayyana cewa, da su aka haɗa kuɗi lokacin da za a gina babban masallacin garin, bayan da al’ummar Musulmi suka nemi gudunmawa a wajensu. Ba su san cewa, wannan taimako da suka bayar zai zo ya zama wurin mafaka a wajensu ba wata rana. Ya maimaita karin magana nan da Hausawa ke cewa, alheri gadon barci. “Malam, mutumin kirki ne. Halinsa daban ne da sauran mutane.”

Wata mata Kirista wacce ta kasance maƙwafciyar Imam, mai suna Ajuji Hamidu, ta bayyana cewa tun suna yara suke tare da iyalin Malam, a gidansa suke rayuwa ba tare da fuskantar wata tsangwama ko kyara ba, sun ɗauke shi kamar uba, saboda yadda ya rungumi kowa ba tare da bambanci ba. Daɓou Gyang mazauni ƙauyen Yelwa ne, kuma ya nuna matuƙar alhininsa bisa rasuwar Imam, inda ya faɗi wata magana game da shi da ta tsaya min a rai. Ya ce, kafin Imam ya kwanta jinya kullum da safe yana fitowa ya riƙa zagayawa yana gaisawa da jama’a, yana tambayar halin da suke ciki. Za su daɗe ba su manta da wannan kyakkyawar halayya ta Malam ba, a cewarsa.

Wata tambaya da ke yawo a bakunan mutane tun bayan samun labarin rasuwar sa ita ce ta, wane ne zai maye gurbin Malam? Wanne hali al’ummar yankin za su kasance a ciki?

Na’ibin Imam, kuma abokinsa, Malam Abdullahi Umar ya tabbatar da cewa, ba za su yi ƙasa a gwiwa ba, wajen cigaba da riƙo da kyawawan halayensa da tarbiyyar da ya yi musu, kuma ba za su bari wani abu ya kawo rabuwar kai a tsakanin su ba. Sai dai sun yi fata da roƙon hukumomi da ƙungiyoyi na duniya da kada su yi watsi da iyalin Malam, da jama’ar Yelwa da Nghar bakiɗaya, gwamnati ta yi ƙoƙari ta cika alƙawarin da ta yi na kai cigaba a yankin, don samun ingantaccen tsaro da zaman lafiya a yankin.

By ukarofi