Zargin juyin mulki: An fitar da sunayen sojojin da abin ya shafa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar Sojoji a ranar Litinin, ta ce za ta maka wasu jami’anta a kotun sojoji bisa zargin su da kitsa makircin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar da ta gabata.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, Hedikwatar Tsaro ta bayar da sanarwar kama wasu jami’an sojoji guda 16 a watan Oktoban 2025 bisa zargin su da ayyukan rashin ladabi da saɓa wa dokokin aiki.

A wata takarda da Daraktan yaɗa labaran hedikwatar, Manjo Janar Samaila Uba ya fitar a Abuja, ya ce tuni aka kammala binciken akan al’amarin, sannan an miƙa rahoton zuwa ofishi na gaba da zai cigaba da aiki a kai.

A cewarsa, za a gurfanar da waɗanda aka samu da laifin a gaban tawagar alƙalan soji kamar yadda dokokin sojoji da wasu na aiki suka tanada.

Rundunar ta kuma jaddada ƙoƙarinta na cigaba da tabbatar da kiyaye ƙa’idojin aiki, biyayya da girmama ikon dokokin ƙasa, kamar yadda sanarwar ta shaida.

Ga jaddawalin waɗanda zargi da hannu a yunƙurin juyin mulkin daga Blueprint: “Brigadier-General Musa Abubakar Sadiq (Nasarawa, 44th Regular Course), Colonel M.A. Ma’aji (Niger, 47th Course), Lt.-Col S. Bappah (Bauchi, 56th Course), Lt.-Col A.A. Hayatu (Kaduna, 56th Course), Lt.-Co l Dangnan (Plateau, 56th Course) and Lt.-Co M. Almakura (Nasarawa, 56th Course).”

Akwai kuma: “Major A.J. Ibrahim (Gombe, 56th Course), Major M.M. Jiddah (Katsina, 56th Course), Major M.A. Usman (FCT, 60th Course), Major D. Yusuf (Gombe, 59th Course), Major I. Dauda (Jigawa, DSSC 38), Captain I. Bello (DSSC 43) and Captain A.A. Yusuf.”

Sauran sune “Lieutenant S.S. Felix (DSSC), Lieutenant Commander D.B. Abdullahi (Navy) and Squadron Leader S.B. Adamu (Air Force)”, kamar yadda jaridar ta ruwaito.

By Babaji