Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Sabbin bayanai sun fito kan yadda komar binciken sojoji ta maƙalo Birgediya Janar Musa Sadiƙ cikin binciken da rundunar sojojin Nijeriya ke yi kan yunƙurin juyin mulki da aka ce an shirya, domin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wani yunƙuri da hukumomi suka ce an daƙile shi tun kafin ya yi nisa.
Rahotanni sun nuna cewa Sadiƙ na cikin jami’an soji 16 da aka kama tare da tsarewa tun watan Oktoban bara bisa zargin hannu a cikin wannan shiri. Daga cikin waɗanda aka kama, 14 daga rundunar sojin ƙasa ne, sai ɗaya daga rundunar ruwa da kuma ɗaya daga rundunar sama. Daga baya kuma bincike ya faɗaɗa inda aka sake cafke wasu jami’ai da fararen hula.
Tun da farko dai rundunar soji ta musanta raɗe-raɗin yunƙurin juyin mulki, tana mai cewa ana binciken jami’an ne kan laifuffukan rashin ɗa’a da karya dokokin aiki. Amma a ranar 26 ga Janairu, Hedikwatar Tsaro ta ƙasa ta tabbatar da cewa bincike ya gano alamun shirin kifar da gwamnati, tare da bayyana cewa duk jami’an da ake zargi za a gurfanar da su a gaban kotun soji.
Majiyoyin tsaro sun shaida cewa zargin da ake yi wa Birgediya Janar Sadiƙ ba wai shi ne jagoran shirin ba ne kai tsaye, sai dai ana zarginsa da samun labarin shirin tun da wuri amma bai kai rahoto ga hukumomin da suka dace ba.
A cewar majiyoyin, ana kallonsa a matsayin wanda ya sani amma bai ɗauki mataki ba, abin da doka da wa’idojin soja ke ɗauka a matsayin babban laifi na rashin bin tsarin aiki.
Wani jami’i da ke da masaniya kan binciken ya ce ana kallon Sadiƙ a matsayin “abokin laifi” maimakon jagora, domin ba a ce ya taka rawa kai tsaye wajen aiwatar da shirin ba.
Birgediya Janar Musa Sadiƙ, mai lambar soja N/10321, an haife shi a ranar 3 ga Janairu, 1974. Ya yi karatu a Kwalejin Horar da Hafsoshin Soji ta Nijeriya (NDA) daga 1992 zuwa 1997 a karkashin Regular Course 44. ɗan asalin jihar Nasarawa ne kuma jami’in rundunar infanteri, inda ya samu ƙarin girma zuwa kanar a 2015 sannan ya zama birgediya janar a 2019. Ya taɓa riƙe muƙaman kwamandan Briged ta 3 a Kano da kuma Garrison Commander na Rundunar 81 a Legas.
Rahotanni sun kuma nuna cewa wannan ba shi ne karo na farko da ake danganta shi da zarge-zarge ba. A shekarar 2024 an taba tsare shi kan zargin rashin ɗa’a mai tsanani, ciki har da karkatar da kayan tallafin abinci da kuma sayar da wasu kayayyakin soja. Duk da cewa waɗannan zarge-zargen sun bambanta da batun juyin mulkin, an ce ana duba tarihin aikinsa gaba daya a yayin binciken da ake yi yanzu.
Hukumomin soji ba su fitar da cikakken bayani a hukumance kan shari’ar Sadiƙ ba, amma sun jaddada cewa za a bi duk matakan doka da ƙa’idoji wajen hukunta duk wanda aka samu da laifi. Shi ma Sadiƙ bai fito fili ya mayar da martani kan zarge-zargen ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
