Hajiya Binta, matar Mamman Shata ta rasu

Spread the love

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Daya daga cikin matan fitaccen mawaƙin ƙasar Hausa, Marigayi Mamman Shata, wato Hajiya Binta Shata ta kwanta dama a ranar Laraba, 28 ga Janairu, 2026.

Bayanin hakan ya fito ne daga ɗaya daga cikin masana rayuwar Marigayi Shata, wato Hussaini Dogo, a kafafen sadarwa, musamman a zauren Makaɗa da Mawaƙa a ranar Laraba.

Ya ce, “Allah ya yi wa ɗaya daga cikin matar Dr. Alhaji Mamman shata Katsina rasuwa, Hajiya Binta, mahaifiyar su Jamila Shata, yanzun nan. Za a yi jana’izarta an jima a ‘Central Mosƙue’ Abuja bayan sallar la’asar. Muna roƙon Allah ya jikan ta da rahama.”
a shekara ta 1999 Allah ya karɓi rayuwar Mamman Shata, mawaƙin da ake kallo a matsayin ba a yi tamkarsa ba a ƙasar Hausa, kimanain shekara a 27 kenan da rasuwarsa, inda ya bar ’ya’ya da jikoki da dama bayan matansa, waɗanda Marigayiya Binta Shata ke cikinsu.

Tuni dai aka yi jana’aizarta kamar yadda addinin Islama ya tanada.

By ukarofi