Majalisar Shari’a na neman a tsige shugaban INEC yayin da CAN a Arewa ta yi ƙememe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wani sabon al’amarin addini da siyasa na neman tayar da hazo a Nijeriya yayin da Majalisar Shari’ar Ƙoli a Nijeriya (SCSN) ta ce ba za ta amince da duk wani zaɓe da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) za ta gudanar ƙarƙashin jagorancin Farfesa Joash Ojo Amupitan ba, lamarin da ya janyo cece-kuce daga ƙungiyoyin Kiristoci da saɓanin ra’ayoyin jama’ar ƙasa.

SCSN ta bayyana haka ne a ranar Laraba yayin gabatar da lakcar gabanin Ramadana ta shekara-shekara da aka yi a Abuja, inda ta yi kira da a gaggauta tsige farfesa Amupitan a muƙamin, tana mai kafa hujja da rashin gamsuwa da nagartarsa.

Da yake jawabi a taron, Shugaban majalisar, Sheikh Bashir Aliyu Umar, ya ce al’ummar Musulmi ba za su taɓa yarda da sahihancin dukkan zaɓukan da za a gudanar a ƙarƙashin jagorancin Amupitan ba sakamakon samun sa da hannun a rubutun shari’ar da ke ayyana Kiristoci a matsayin waɗanda ta’addanci ke shafa a Nijeriya.

A cewarsa, gabatar da rubutun shari’ar mai shafi 80 da Amupitan ya yi akan batun, abu ne da ke barazana ga haɗin al’ummar ƙasa musamman ga waɗanda ke neman kare harkokin dimukraɗiyyar Nijeriya.

”Har yanzu muna kan bakarmu, saboda shi shugaban hukumar zaɓe bai fito ya musanta cewa wannan abun ba haka ba ne. Ya na nan kan iƙirarinsa, bai ma ga cewa wannan wani abu ne da zai fito ya yi magana a kai ba”, inji Sheikh Umar.

Gwamnatin Tarayya ta sha musanta batun yi wa Kiristoci kisan gilla a Nijeriya tun bayan da Amurka da ayyana ƙasar a matsayin wadda ake da damuwa akanta saboda zargin tauye ‘yancin Kiristoci, lamarin da Nijeriyar ta bayyana a matsayin abin ka iya haddasa rarrabuwar kai acikin al’ummarta.

A wani labarin kuma, Ƙungiyar Kiristoci ta ƙasa, CAN, reshen Arewa, ta ƙi amincewa da kiran da SCSN ta yi na a tsige Farfesa Joash Amupitan a shugabancin INEC.

Kamar yadda jarida Vanguard ta ruwaito a yau Juma’a, Shugabannin Kungiyar CAN na Arewacin Nijeriya sun nuna goyan bayan su ga Amupitan shugaban hukumar zaɓe ta kasa INEC duk kuwa da kasancewar sa cikin waɗanda suka yi kira ga Amurka da ta kawo ɗauki ga Kiristocin ƙasar da ake yiwa kisan ƙare dangi.

By Babaji