
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An shiga kokwanto a Jihar Zamfara game da rashin bayyanar matashin yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima da ke yaɗa manufofinsu da na jam’iyyar APC ta Soshiyal Mediya, wato Bashir Isa Gusau, wanda ake zargin kodai ‘yan bindiga sun sace shi ko kuma jami’an tsaron da aka alaƙanta wa gwamnatin jihar.
Tun a daren ranar Laraba wayewar Alhamis Isa Gusau, wanda sanannen matashin yaɗa manufofin APC ta kafafen sada zumunta ne, ya yi ɓatan dabo, lamarin da ya tada yamutsi acikin al’ummar jihar.
A wata sanarwa da APC reshen jihar ta fitar wa manema labarai, jam’iyyar ta yi zargin cewa wasu jami’an tsaron da aka alaƙanta da aiki da Gidan Gwamnatin jihar a Guda ne suka kama shi.
A cewarta, Sakatarenta yaɗa labaranta, Yusuf Idris Gusau ya ce al’amarin ya auku ne da misalin ƙarfe 10 na dare yayin kallon wasannin Champions League a wani gidan kallo da ke Sabon Gari acikin Gusau.
Jam’iyyar ta yi zargin cewa mutane huɗu da suka bayyana kawunansu a matsayin jami’an tsaron daga gidan gwamnatin ne suka je a wata motar da ke ɗauke da rufaffen allon lamba suka tilasta wa matashin tafiya tare da su.
Haka kuma ta yi zargin cewa, a lokacin da sauran ‘yan kallon suka yi yunƙurin kawo masa ɗauki, sai jami’an suka riƙa harbe-harbe a sama domin tarwatsa su kana daga bisani suka yi awon-gaba da matashin.
Jam’iyyar ta kuma zargi gwamnatin jihar da takura wa ‘yan ɓangaren adawa da cin fuskan ga ikon shugabanci na gari.
Tuni ta ce, ta sanar da lauyoyinta da kuma yin ƙorafi ga Sufeto Janar na ‘yan sanda da Hukumar DSS, inda ta nemi da a gudanar da bincike.
