Kotu ta soke babban taron PDP na Ibadan

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babbar kotun tarayya da ke Ibadan a Jihar Oyo, ta soke babban taron da jam’iyyar adawa, PDP ta gudanar a ranar 15 ga watan Nuwamba, 2025.

A yayin taron ne kuma aka zaɓi Tanimu Turaki a matsayin shugaban jam’iyyar.

Kotun ta kuma haramta wa Turaki da wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar cigaba da bayyana kansu a matsayin shugabanin PDP a matakin kasa.

A hukuncin da kotun ta yanke, an tabbatar da cewa kwamitin riƙon ƙwarya na jam’iyyar, wanda Sanata Samuel Anyanwu ke jagoranta, shi ne kaɗai halastaccen kwamitin gudanarwa na PDP har sai an gudanar da babban taron ƙasa da doka ta amince da shi.

Duk da cewa an samu wakilci daga jihohi 36 da Abuja na faɗin Nijeriya da suak halarci taron, an samu tsaikon rashin amincewa akan karɓa-karɓa, jinkirin tantancewa da zargin zagon-ƙasa ga tsagin jam’iyyar.

By Babaji