Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Kungiyar ’Yan Kasuwar ƙaramar Hukumar Kabo mazauna waje, wadda aka fi sani da Kabo Zone Traders Association (KAZTA), ta karɓi jakadun zaman lafiya daga cibiyar Wazobia Conflict Resolution and Peace Advocacy Initiative (WACORPAI), ƙarƙashin jagorancin Dakta Garba Sulaiman Marafa.
An miƙa lambar yabo ne a wani babban taro da ƙungiyar KAZTA ta shirya a garin Kabo, Jihar Kano, a ranar Asabar da ta gabata, wanda ya samu halartar manyan baki daga sassa daban-daban na jihar.
Daga cikin waɗanda aka karrama akwai Shugaban ƙaramar Hukumar Kabo, Hon. Lawan Najume; Sarkin Fulani Masanawa, Alhaji Yusuf Khan Umma; Sarkin Matasan Kabo, Alhaji Hashimu; Shugaban ƙungiyar KAZTA na ƙasa, Adamu Salisu Kabo; da Sakataren Yaɗa Labarai na ƙungiyar, Alhassan Ibrahim.
A jawabinsa, Shugaban WACORPAI, Dakta Garba Sulaiman Marafa, ya bayyana cewa an zaɓi waɗannan mutane ne bisa gudunmawar da suka bayar wajen tabbatar da zaman lafiya, tsaro da bunƙasa tattalin arziki. Ya ce irin wannan aiki yana taimakawa rage rikice-rikice da ƙarfafa zaman tare a tsakanin al’umma.
Ya ƙara da cewa WACORPAI za ta ci gaba da haɗin gwiwa da ƙungiyoyi irin su KAZTA domin wayar da kan jama’a kan muhimmancin zaman lafiya, musamman a ƙananan hukumomi da ke buƙatar ƙarfafa fahimtar juna tsakanin jama’a.
ƙungiyar KAZTA ta kuma karrama wasu fitattun mutane da suka taka rawa a fannoni daban-daban, ciki har da Malam Zakari Dahiru a fannin ilimi, Jummai Ayuba (DPO) a fannin tsaro, Dakta Ibrahim Gwarzo a fannin lafiya, da Ado Talle Abubakar Akilu a fannin kasuwanci.
A cewar shugabannin ƙungiyar, irin wannan karramawa na ƙara zaburar da al’umma wajen bayar da gudunmawa ga ci gaban yankinsu, tare da ƙarfafa zumunci da haɗin kai a tsakanin ’ya’yan Kabo mazauna ciki da wajen ƙasa.
Shugaban rukunonin kamfanonin Zangon Kabo Pharmacy da Travelling Agency, Alhaji Bashir Abdulrahman, ya yaba da yadda ’ya’yan Kabo ke haɗa kai domin tallafa wa garinsu ta hanyoyi daban-daban.
A ƙarshe, Shugaban KAZTA, Adamu Salisu, ya ce ƙungiyar za ta ci gaba da ɗaukar nauyin shirye-shiryen raya al’umma, tare da godiya ga dukkan waɗanda suka taimaka wajen nasarar taron.
