Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Kwamishinoni biyar da wasu manyan jami’an gwamnatin Jihar Kano goma sun ajiye mukamansu, tare da jaddada mubaya’a da biyayya ga Jagoran Kwankwasiyya, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, a yayin da rikicin siyasa ke kara daukar zafi tsakanin sa da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf.
Binciken da Manhaja ta gudanar ya nuna cewa daga cikin kwamishinonin da suka yi murabus akwai Mustapha Rabiu Kwankwaso, Kwamishinan Matasa da Wasanni; Dakta Yusuf Kofar Mata, Kwamishinan Kimiyya da Fasaha; Nasiru Sule Garo, Kwamishinan Ayyuka na Musamman; Adamu Kibiya, Kwamishinan Jinkai; da AVM Ibrahim Umar (mai ritaya), Kwamishinan Tsaro.
Haka kuma, wasu manyan jami’an gwamnati goma sun ajiye mukamansu, ciki har da Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabiu; Shugaban Gidan Zoo, Hon. Sadik Kura Muhammad; Shugaban Hukumar Gyaran Tituna, Alhaji Hassan Danbaffa; da Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Kasuwar GSM, Hon. Sani Shehu Makarya.
Sauran sun hada da Hajiya A’in Jafaru Fagge, Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Yada Kyakkyawan Sako; Mujittafa Muhammad Auwalu, Jami’in Alhazai na Karamar Hukumar Gwale; Hon. Nafiu Umar Dan Kura, SSA Protocol Abuja; Aminu Sa’idu Meenan Kwankwasiyya; da Shafa’atu Ahmad Landan, B.E.
A cikin bayanan murabus dinsu, jami’an sun bayyana cewa sauye-sauyen siyasa da rikice-rikicen da suka kunno kai a jihar ne suka tilasta musu daukar wannan mataki, tare da jaddada aniyarsu ta ci gaba da mara wa tafiyar Kwankwasiyya baya karkashin jagorancin Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.
