Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Jihar Ogun na daf da shiga sahun jerin jihohin da ke samar da danyen mai a Nijeriya bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da fara haƙo mai na kasuwanci a yankin Eba da ke ƙaramar Hukumar Ogun Waterside.
Gwamnan jihar, Dapo Abiodun, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake karɓar baƙuncin Babban Kwamandan Rundunar Sojin Ruwa na Yankin Yamma, Rear Admiral Abubakar Abdullahi Mustapha, tare da manyan jami’ansa, a ofishinsa da ke Oke-Mosan a Abeokuta.
Gwamnan ya kuma sanar da cewa Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta fara aikin gina tashar jiragen ruwa ta Olokola Deep Seaport da ke ƙaramar hukumar Ogun Waterside, wani gagarumin aiki da aka daɗe ana jira tsawon shekaru.
A cewarsa, waɗannan manyan ayyuka biyu na daga cikin abubuwan da shugaban ƙasa ya ba muhimmanci na musamman.
Ya bayyana cewa tashar jiragen ruwan Olokola za ta taimaka matuƙa wajen rage cunkoso a tashoshin jiragen ruwa na Legas, yayin da haƙo ɗanyen mai a tsibitin Tongeji zai bunƙasa tattalin arziki tare da kawo cigaba ga yankunan bakin teku.
“Zan so na sanar da ku cewa Shugaban ƙasa ya amince da fara aikin haƙo ɗanyen mai na kasuwanci a Tongeji Island, kuma nan gaba kadan za a fara ganin ayyuka suna kankama a yankin,” inji gwamnan.
Ya ƙara da cewa, aikin tashar jiragen ruwan Olokola, wanda ya daɗe yana kan takarda ba tare da aiwatarwa ba, yanzu ya dawo kan turbar gaskiya sakamakon goyon bayan shugaban ƙasa. A cewarsa, a cikin makonni biyun da suka gabata kadai, an gudanar da taruka da dama kan yadda za a tabbatar da ganin aikin ya fara gudana cikin gaggawa.
Gwamna Abiodun ya ce shugaban ƙasa ya nuna sha’awa ta musamman ganin cewa aikin tashar jiragen ruwan ya kai wani mataki mai a zo a gani tsakanin yanzu da shekara mai zuwa, musamman ganin yadda sabon titin bakin teku zai samar da wata hanya ta daban wajen jigilar kaya.
Ya kuma bayyana cewa, sabuwar tashar jiragen ruwan za ta kasance da suna Blue Marine Economic Zone, domin nuna muhimmancin yankin na tattalin arziki da kasuwanci bisa matsayinsa na bakin teku.
Gwamnan ya yaba wa Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya bisa kafa sansanin aiki na musamman a Tongeji Island, yana mai cewa kasancewar sojojin ruwan a yankin zai taimaka wajen hana shigar masu aikata laifuka daga makwabciyar ƙasar Benin tare da kare iyakokin Nijeriya.
Haka kuma ya ce, gwamnatinsa na ƙoƙarin samar da muhimman ababen more rayuwa ga mazauna yankin domin inganta rayuwarsu da kuma tallafawa sabbin damammakin tattalin arziki da za su taso sakamakon waɗannan ayyuka.
A nasa jawabin, Rear Admiral Mustapha ya bayyana Jihar Ogun a matsayin wuri mai matukar muhimmanci ga tsaron ƙasa, yana mai cewa za a kara ƙarfafa sansanin sojin ruwan da ke Tongeji Island saboda muhimmancin yankin wajen hako mai.
Ya ce ziyarar ta su na da nufin ƙara danƙon zumunci da hadin gwiwa tsakanin Rundunar Sojin Ruwa da Gwamnatin Jihar Ogun domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin.
