Yara fiye da 1000 gidauniyar Gwagware ta ɗauki nauyin yi masu kaciya

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban ƙungiyar kwamred Mannir Suleiman ya faɗi haka a lokacin da yake duba gyaran sabon ofishin gidauniyar a Katsina.

Ya ce nan bada jimawa ba gidauniyar za ta fara raba kayan yaran makarantun firamare a ƙananan hukumomi 34 da ke jihar.

Kayan sun haɗa da rigunan makaranta, littafin rubutu da alli na rubuta da za su zagaya da kansu zuwa ƙananan hukumomin domin raba wa yara marasa ƙarfi da masu buƙata ta musamman inji Mannir.

“Duk waɗannan ayyuka da Gidauniyar Musa Adamu Funtua ke yi daga ajihummu muke,”kwamred ya ce .

Ya ce suna wannan hidimar ce ganin irin abubuwan alheri da Musa Adamu ke yi na raya kasa da tallafawa al’umma ba ma a yankin Funtua kaɗai ba har da jihar Katsina baki ɗaya.

Kwamred Mannir Suleiman ya ce gidauniyar ta yaba da salon shugabanci da Hon Musa Adamu ke nunawa a matsayin sa na kwamishinan lafiya a jihar.

‘Babu shakka gwamna Dikko Raɗɗa bai yi zaɓen tumun dare da ya naɗa Musa Adamu Funtua kwamishinan lafiya a jihar,”Mannir ya ce.

Haka kuma Gidauniyar ta jinjina wa gwamnatin Dikko Raɗɗa kan yadda ta fito da jihar Katsina a idon duniya ta hanyar aiwatar da ayyukan raya ƙasa bama a yankin Funtua har da jiha baki ɗaya.

Ya ce shirye shirye ya kankama wajan buɗe sabon ofishin Gidauniyar Katsina wanda a cewar sa suna sa ran Hon Musa Adamu Funtua zai jagoranci buɗe wa.

By ukarofi