DAGA JOHN WADA a Lafia
Wata ƙungiyar siyasa da aka fi sani da Nasarawa North Peace Assembly a turance da ke jihar Nasarawa ta buƙaci jam’iyar APC mai ci a jihar ta tabbatar ta bar zaɓen fitar da gwanin ta na kujerar gwamnan jihar na shekarar 2027 a bude ga duk wanda ya cancanta ba tare da yin la’kari da shiyar da ya fito ba.
Ƙungiyar ta bayyana haka ne ta bakin shugaban ta Hon. Isah Nathaniel JP a lokacin wani gangamin wayar da kai na musamman da ta shirya wa ɗan takarar gwamnan jihar a inuwar jam’iyyar APC a zaɓen 2027 dake tafe wato tsohon shugaban rundunar ‘yan sandan Nigeria, Mohammed Abubakar Adamu (Mai ritaya) a yankin Nasarawa ta Arewa a cikin garin Akwanga.
Yace kiran ya zama wajibi idan akayi la’akari da yadda wasu ke cigaba da yaɗa cewar yakamata jam’iyyar APC ɗin ta mai da kujerar gwamnan jihar ta Nasarawa wa shiyar Yammacin jihar.
A cewar Hon. Nathaniel a yanzu haka, kowanne shiya a jihar ya riga ya fito da gwamna ya kuma yi, a yanzu abinda ya rage shine a bai wa kowa damar fitowa takarar na 2027 ba tare da nuna son zuciya ba.
Yace sanin kowa ne cewa cikin dukan masu neman kujerar na gwamnan jihar a APC, shi Mohammed Abubakar Adamu ne yafi cancanta da ƙwarewa da idan jam’iyyar ta kuskura ta hana shi tikitin to tabbas za ta iya rasa kujerar kwata-kwata ga jam’iyyun adawa.
Shugaban ƙungiyar siyasar ya ƙara da cewa batun tsarin karɓa-karɓa wato zoning a turance a jihar baya cikin doka kuma ba ya haifar da ɗa mai ido don haka bai kamata jam’iyyar APC mai ci a jihar ta ba da fifikon ta ga tsarin ba.
Daganan sai Hon. Isah Nathaniel ya jinjina wa ‘yan’yan jam’iyyar a shiyar Nasarawa ta Arewar da keyawen ta musamman magoya bayan ɗan takarar Mohammed Abubakar Adamu da suka fito ƙwan su da kwarkwata don nuna goyon bayan su ga tsohon shugaban ‘yan sandan Nijeriya ɗin ta halartan gangamin wayar da kan zuwa lungu-lungu da saƙo-saƙon yankin da kewayenta baki ɗaya.
A yanzu haka dai wakilin mu ya binciko cewa kimanin ‘yan takarar kujerar gwamnan jihar Nasarawa ɗin 22 ne suke nema a inuwar jam’iyyar APC a jihar.
