Iran ta ayyana sojojin Ƙungiyar Tarayyar Turai a matsayin ‘yan ta’adda

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Iran ta ayyana sojojin Tarayyar Turai (EU) a matsayin ƙungiyar ta’addanci kwanaki kaɗan bayan EU ta ayyana rundunar kare juyin juya halin ƙasar ta IRGC da ƙungiyar ta’addaci.

Kakakin majalisar dokokin ƙasar ya sanar da haka a ranar Lahadi, bayan matakin da EU ta ɗauka na yin amfani da wannan sanarwar ga dakarun kare juyin juya halin Musuluncin ƙasar a ‘yan kwanakin nan.

An ga yadda yan majalisar suka sanya koren rigar masu gadi a wani nuni na haɗin kai a zaman majalisar inda suka yi ta rera taken “Mutuwa ga Amurka”, “Mutuwa ga Isra’ila,” da kuma “Kunya a gare ku Turai”, kamar yadda gidan talabijin na kasar ya haska wa duniya.

Da yake jawabi akan matakin da ƙungiyar ta ɗauka, Kakakin majalisar, Mohammad Bagher Ghalibaf ya ce a ƙarƙashin “Mataki na 7 na dokar yaƙi da ayyana IRGC a matsayin ƙungiyar ta’addanci, ana ɗaukar sojojin kasashen Turai a matsayin kungiyoyin ‘yan ta’adda”.

A shekarar 2019 ne aka fara zartar da dokar a lokacin da Amurka ta sanya jami’an tsaro a matsayin ƙungiyar ta’addanci.

An gudanar da zaman na yau Lahadi ne a daidai lokacin da ake cika shekaru 47 da dawowa daga gudun hijirar marigayi Ayatullah Ruhollah Khomeini wanda ya kafa Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shekarar 1979.

By Babaji