Atletico Madrid ta saye Ademola Lookman daga Atalanta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ɗan wasan gaba na Super Eagles, Ademola Lookman ya kammala koma wa ƙungiyar Atletico Madrid, lamarin da ke nuna wa’adinsa a Atalanta da ke ƙasar Italiya ya zo ƙarshe.

An yi musayar ɗan wasan ne akan kuɗi Yuro miliyan 40 bayan shafe tsawon makonni ana tattaunawa a tsakanin ƙungiyoyin biyu da kuma ɗan wasan.

Atletico Madrid ta daɗe tana nuna kwaɗayin sayen ɗan wasan inda ta sha fuskantar gasa daga Fenerbahçe ta ƙasar Turkiyya, wadda da fari ya ƙulla amincewar baka da ita amma daga baya Atletico ta yi nasarar sayo shi.

An samu tsaikon komawarsa Fenerbahçe ne akan tsare-tsaren biya, inda hakan ya ba At. Madrid damar shiga cinikin tare da yarje wa buƙatar Atalanta akan ɗan wasan.

A yanzu dai Lookman mai shekaru 28 zai sake haɗuwa da tsohon kocinsa, Luciano Spalleti, wanda suka yi aiki tare a lokacin da Napoli ta lashe gasar Serie A.

Ana fatan wannan ci-gaba zai taimaka wa sabuwar ƙungiyar ɗan wasan wajen ƙarfafa wa ƙarfinta na kai hari musamman ganin yadda yake nuna bajinta a wasannin gida da na Turai.

By Babaji