Bambancin so da soyayya

Spread the love

Daga MOHAMMED BALA GARBA

Wasu sun ɗauka da ‘So’ da ‘Soyayya’ duk abu ɗaya, sai dai ba haka abin yake ba. Ita Soyyaya aiki ce (verb); yayin da So kuma wani abu ne mai zaman kansa (independent), wanda wani lokacin shi yake samar da Soyayya. Amma kafin nan, bari mu yi duba ga yadda wasu suka ba da ma’anonin su.

Ma’anar so.

-So – wani sauki ne na zuci da ke ziyarar masoya guda biyu ba tare da ya shawarce su ba. ~ Aisha Abdullahi Muhammad 

-So – wata iska ce mai yawo wanda babu wani ɗan adam ko dabba da bai shake ta ba. ~ Wikipedia.

-So – buƙata ko ƙaunar juna, musamman mace da namiji. ~ ƙamusun, Jami’ar Bayero, Kano.

Ma’anar soyyaya:

-Soyayya – wata babbar ji ce da take mamaye zuciyar dan Adam tun farkon halittarsa. ~ Shafin Masoya.

-Soyayya – nuna ƙauna daga ɓangarori biyu na masu ƙaunar juna, musamman mace da namiji. ƙamusun, Jami’ar Bayero, Kano.

-Soyayya – tana nufin ‘yan karairayi da ake aika wa juna domin sanya farin ciki. ~ Mohammed Bala Garba.

Idan muka yi duba ga waɗannan ma’anoni mabambanta, za mu iya fahimtar so daban yake da soyyaya. Domin za ka iya son wanda ba soyayya ku ke ba, saɓanin Soyyaya, da zai yi wuya ki yi soyyaya da wanda ba son shi kike ba. Don haka, So shi ne ran da ke samar da Soyayya a wasu lokutan; saboda wanda kike ƙi zai yi wahala ya samu Soyayya daga gare ki.

Na yi nan.

Mohammed Bala Garba manazarci kuma marubuci ne daga Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno,

20 ga Junairu, 2026

By ukarofi