Manoman Zariya sun koka kan ƙwace musu gonakin da sojoji suka yi

Spread the love

Daga MOH BELLO HABIB a Zariya 

Manoman rani dake Gyallesu da maƙwabtaka da Cibiyar Horas da Kuratan Sojoji (Depot Nigerian Army) dake Zariya cikin jihar Kaduna sun koka akan abin da suka kira zalunci da mahunta makarantar suka yi na gonakin da suka gada daga kakannin su sama da shekaru 150 da suka gabata.

Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala sallah da adu’o’i na musamman da manoman suka gabatar don neman taimakon ya ƙwato masu gonakinsu kimanin 500 da sojoji suka yi tare da shigar cikin haraban barikinsu, mai magana da yawun manoman, Malam Musa Muhammad ya ce wannan zaluncin na sojojin ya jefa sama da manoma 5000 cikin mawuyacin hali na rashin abin yi tare gurgunta tattalin arzikisu.

Malam Musa ya ce sun shigar da ƙara a gaban Babban Kotun Jihar dake Dogarawa wanda mai shari’a Kabir Dabo ke jogaranta akan magana yau shekaru shida kenan.

Mai maganar da yawun manoma ya ƙara da cewa a shekarar 2019 kotun ta dakatar da sojoji daga shiga taɓa gonakin ya zuwa lokacin da yadda shari’ar ta kaya amma sojojin suka ƙi bin hukuncin kotun.

Da yake ƙarin bayani aka lamarin, Limamin da ya jagoranci sallan, Malam Muhammad Bashir ya ce a tsawon rayuwan shi sama shekaru tamanin wannan shine zaluncin sojoji da ya gani.

Ya yi kira ga gwamnatoci da masu ruwa da tsaki su taimaka masu don karɓo masu gonakinsu daga sojoji, “saboda ba su da wata sana’a sai noma amma ga shi ƙiri-ƙiri an zalunce su.”

By ukarofi