Gidauniyar Gwagware Musa ta yi ta’aziyar mutanen da ‘yan bindiga suka kashe a Doma

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban Gidauniyar kwamred Mannir Suleiman ya faɗi haka a wata takardar da ya fitar wanda aka rabawa manema labarai a Katsina.

Ya ce mutuwar waɗannan bayin Allah ba ƙaramin asara bane ga al’ummar jihar Katsina har da ƙasa baki ɗaya.

Ya ce gidauniyar ta nuna alhinin kan waɗannan mutane da basu ji ba basu gani kawai ‘yan bindiga su buɗe masu wuta ba tare da dalili ba.

Sun kashe masu ruwa da tsaki na garin tare da ƙona gidaje,kasuwanni makarantu da sauran muhimman wurare don rashin imani.

Kwamred Suleiman yayi fatan Allah mayar masu da sabon arziki da juriyar rashi da suka yi na iyali, yan uwansu da sauran mutanen gari da yan bindiga suka kashe.

Shugaban Gidauniyar ya kuma yaba da yadda gwamnatin jihar Katsina ta tada tawaga mai ƙarfi karkashin sakataren gwamnatin jihar Barista Abdullahi Garba Faskari da shugabannin jami’an tsaro na jihar suka yi masu ta’aziya a madadin gwamnatin jihar.

Haka kuma ya yaba da tallafin kuɗi na rabin miliyan da aka iyalan waɗanda suka rasa ransu.

Kwamred Suleiman sai yayi kira ga mawadata a jihar da su kawowa al’ummar garin Doma ɗauki da tallafin kayan abinci,da kuɗi domin gina da gyara inda aka lalata.

Ya ce babu shakka al’ummar garin Doma na neman taimako na gaggawa, domin haka ya zama wajibi ga masu hali da sauran al’ummar jihar su taimaka cikin gaggawa don inganta rayuwar garin.

Shugaban Gidauniyar ya kuma yi kira da jami’an tsaro ƙara ƙaimi wajen yaƙi da waɗannan yan ta’adda.

By ukarofi