Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta yanke hukuncin ɗaurin shekaru 490 ga tsohon Manajan Darakta na Bankin Fitar da Kaya da Shigo da Kaya na Nijeriya (NEXIM), Robert Orya, bayan samunsa da laifi a kan zarge-zargen badaƙala da suka kai kimanin Naira Biliyan 2.4.
Alƙalin kotun, Mai shari’a F.E. Messiri, ne ya yanke hukuncin bayan ya tabbatar cewa masu ƙara sun gabatar da hujjoji gamsassu da suka tabbatar da laifuffuka 49 da suka shafi cin amanar ofis, haɗa baki da kuma karkatar da kuɗaɗen gwamnati.
Kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 10 kan kowanne laifi, inda aka umarci hukuncin ya gudana a jere, abin da ya kai jimillar shekaru 490 a gidan yari.
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ce ta shigar da ƙarar ta hannun lauyanta, Samuel Ugwuegbulem. Hukumar ta shaida wa kotu cewa laifuffukan sun faru ne a lokacin da Orya ke riƙe da muƙamin Manajan Darakta na NEɗIM tsakanin shekarun 2009 zuwa 2016, lokacin da aka ɗora masa alhakin kula da kuɗaɗen jama’a domin bunƙasa fitar da kayayyakin da ba na mai ba daga Nijeriya.
A cewar EFCC, Orya ya yi anfani da muƙaminsa wajen karkatar da kuɗaɗen bankin ta hanyoyin da suka saɓa wa dokoki da ƙa’idojin harkokin kuɗi, lamarin da ya haifar da babbar asara ga gwamnati.
A cikin hukuncin, alƙalin ya bayyana cewa hujjojin takardu da shaidun da aka gabatar sun nuna a sarari yadda aka gudanar da mu’amaloli ba bisa ƙa’ida ba, inda ya yi watsi da hujjojin kariyar da ɓangaren wanda ake ƙara ya gabatar.
Kotun ta jaddada cewa laifin ya kasance babban cin amanar jama’a, musamman ganin muhimmiyar rawar da NEɗIM ke takawa wajen tallafa wa ɓangaren fitar da kaya domin rage dogaro da man fetur a tattalin arzikin ƙasa.
A baya, an san Orya da ƙoƙarin da ake ganin ya yi wajen inganta ayyukan bankin da bunƙasa tallafin fitar da kaya. Sai dai EFCC ta dage cewa a bayan waɗannan matakai, ana gudanar da karkatar da kuɗaɗe ta ɓoye, abin da ya saɓa wa manufar bankin.
Wannan hukunci na zuwa ne a daidai lokacin da EFCC ke ci gaba da gurfanar da manyan jami’an gwamnati da shugabannin hukumomi bisa zargin cin hanci da rashawa. Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ɓangaren kariyar Orya bai bayyana ko zai ɗaukaka ƙara kan hukuncin ba.
