Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kasurgumin ɗan bindiga, Bello Turji, ya sako jagoran ’yan bindiga da ya jagoranci sulhu da al’ummomin Jihar Katsina, Abdu Lankai.
Bayan Turji ya kama Abdu Lanaki da kwanaki biyar ne ya sako shi bayan sanya bakin wasu shugabannin Fulani.
Manhaja ta samu rahoto cewa a yammacin ranar Litinin magoya bayan Lankai suka, suka tarbe shi a bisa babura.
Abdu Lankai ya fada tarkon su Turji ne a ranar Larabar satin da ya gabata bayan wata gayyata da suka yi mashi da sunan yadda za a yi sasanci a yankin Zamfara inda shi Turji yake cin karensa babu babbaka.
Amsa goron gayyatar da ya yi, ya kai shi shiga hannunsu bisa wasu zarge-zarge da suka yi mashi, ciki har da zargin hana rayansu shigowa yankin Jibiya a yayin da suka yi wata ɓarna a wani wuri.
Har ila yau, wasu majiyoyi da suka nemi a sakaya sunayensu a garin Jibiya sun shaida wa wakilinmu cewa akwai badakalar kuɗin sayen makamai a tsakanin ɓangarorin biyu.
Su Turji sun yi zargin an ba wa Lankai kudi sama da Naira milyan arba’in domin ya sayo masu makamai amma ya rike kudin bai sayo ba, shi ya sa suka yi mashi gadar zare ya kuma faɗa ciki.
Kama Lankai da su Turji suka yi ya jefa jama’ar yankin Jibiya da wani sashe na Batsari cikin zullumi musamman a kan hasashen watsewar shirin sasanci da sulhun da aka yi da ’yan ta’adda. Sulhun da jama’ar suka ga ya haifar masu da kyakkyawan sakamako da kuma samun zaman lafiya.
“Abin da muke jin tsoro shi ne, wargajewar wannan sasanci domin da ma akwai wasu da ba su ji daɗin yin shi ba. To shi Lankai ya tsaya tsayin daka wajen ganin sulhun ya ɗore. Sannan ya tsare duk wata yarjejeniyar da aka shirya a tsakani,” inji wani mazaunin garin Jibiya.
Lankai dai ya kwana gidan shi dake Mallamawa a can yankin Jibiyar, sai dai abin da ba mu samu cikakken bayani a kai ba har zuwa kammala rubuta wannan rahoto shi ne, shin wace matsaya suka cimma musamman.
