Juyin mulkin da aka yi yunƙurin yi an shirya shi ne tun kafin rantsar da Tinubu – Ministan tsaro

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana cewa an fara shirya juyin mulki a Nijeriya tun kafin rantsar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Musa ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Sunday Politics na tashar Channels Tɓ, inda ya ce mafi yawan wadanda ake zargi da hannu a shirin an kama su. 

Ya ce lamarin ya samo asali ne daga wani kanar da ya fusata saboda rashin karin girma, wanda daga baya ya jawo wasu jami’ai da suka nuna rashin jin dadi da mukamansu.

Ministan ya ce shi ma yana cikin wadanda aka nufa da kamawa a lokacin shirin, amma ya jaddada cewa wadanda suka shirya juyin mulkin ba su fahimci girman abin da suka shiga ba, yana mai cewa ’yan Nijeriya da rundunar soji za su yi turjiya ga duk wani yunƙurin kifar da dimokuraɗiyya.

Ya ƙara da cewa binciken lamarin ya gudana ne a hankali domin tattara hujjoji, tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro da leken asiri daban-daban. 

A cewarsa, duk wanda ake zargi da hannu a lamarin za a ci gaba da bibiyarsa, ciki har da waɗanda ake zargin suna da alaƙa da siyasa.

Musa ya kuma jaddada cewa rundunar sojin Nijeriya ta ƙara tsaurara matakan ladabtarwa da sa ido domin hana aukuwar juyin mulki, yana mai cewa a halin yanzu abu ne mai matuƙar wahala a aiwatar da irin wannan yunƙuri a ƙasar.

By ukarofi