Akwai yiwuwar hukuma ta kama ni a kowane lokaci – El-Rufa’i

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa akwai yiwuwar a kama shi a kowane lokaci daga ɓangaren hukumomin tsaron Nijeriya.

El-Rufai, wanda jigo ne a jam’iyyar adawa ta ADC, ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar BBCHausa a ranar Laraba, inda ya yi zargin cewa ana tilasta wa ‘yan siyasa sauya sheƙa zuwa cikin jam’iyya mai mulki (APC).

El-Rufa’i, wanda a baya-bayan nan ya kara matsawa wajen sukar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da kuma jam’iyyar APC da ya yi mulki a ƙarƙashinta na tsawon shekaru takwas, ya ce duk da cewa har yanzu ba a kama shi ba, tuni aka aka riga aka tsare wasu daga cikin makusantansa.

“Mutane huɗu da muka yi aiki tare da su a Kaduna an kama su; don haka batu ne na lokaci kawai kafin su zo kaina ma”, inji tsohon gwamnan.

Kalaman na El-Rufai na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da tsarewa da gudanar da shari’ar tsohon Antoni Janar kuma Ministan Shari’a na Ƙasa, Abubakar Malami, wanda har yanzu ke hannun hukuma.

Malami na fuskantar tuhume-tuhume da dama ciki har da batun zargin sa da sauya akalar wasu maƙudan kuɗaɗe da Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin EFCC ta gabatar akansa.

Daga bisani, Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, ta sake kama shi bisa zargin sa da hannu a ɗaukar nauyin ta’addanci.

By Babaji