Alaƙar da ke tsakanin rubutun adabi da aikin jarida alaƙa ce irin ta Ɗanjuma da Ɗanjummai – Umar Yunus Jos

Spread the love

“Dlilin da ya ja hankalin maza suka duƙufa rubuce a baya nake fatan ya dawo nan gaba”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Harkar rubutun adabin Hausa, harka ce mai faɗin gaske wacce ta tattaro mutane daban-daban, daga ɓangarorin ilimi da rayuwa mabambanta. Ba mamaki ba ne ka ga malamin makaranta marubuci, ko jami’in tsaro, ɗan siyasa, injiniya, lauya ko likita da sauransu, suna ba da gagarumar gudunmawa cikin harkar rubutun adabi. Umar Yunus na daga cikin irin waɗannan fasihan mutane waɗanda ke bai wa adabi gudunmawa a ɓoye da zahiri, duk da kasancewar sa ɗanjarida, kuma malamin makaranta, mai sha’awar harkokin wasannin motsa jiki. Ba da jimawa ba ya samu damar fitar da littafinsa na farko da ya wallafa, ‘Yi Wa Wani Yi Wa Kai’, bayan rubuce-rubuce da yake yi yana ajiyewa. A ganawarsa da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, marubucin ya bayyana masa abin da ya ba shi sha’awar shiga fagen adabi da aikin jarida. A yi karatu lafiya. 

MANHAJA: Ka gabatar mana da kanka.

UMAR YUNUS: Sunana Umar Yunus. An haife ni a garin Jos, babban birnin Jihar Filato, a wata anguwa mai suna Nasarawa da ke ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa.  Na yi makarantar firamare da sakandire da jami’a duk a Jos. Ni ɗan jarida ne a ɓangaren aikin rediyo, ni marubucin adabi, marubucin waƙoƙin Hausa, kuma malamin makaranta. Sannan kuma ina ɗan taɓa harkokin kasuwanci. Ina da aure da iyali. Alhamdulillah. 

Ko za ka gaya mana wacce irin rayuwa ka taso a cikinta wacce ta mayar da kai mutumin da ka zama yanzu?

Ni ne ɗa na uku a gidanmu, saboda haka akwai abubuwa da dama game da rayuwa da na fahimta tun ina matakin sakandire. Na fahimci cewa wajibi ne mutum ya dogara da kansa idan yana so ya tsira da mutuncinsa; kuma hakan ya taimaka min yayin da nake tasowa har zuwa yanzu.

Wanne irin gida ka taso kuma wacce tarbiyya ka samu daga wajen iyayenka wanda yanzu ka ke alfahari da ita?

Na taso a gidan da ba a ƙyale yaro ya yi gaban kansa. Iyayenmu da yayunmu sun saka ido sosai a kanmu wajen ganin ba mu kauce daga kan hanyar da suka ɗaura mu ba. Duk da mun sha zamewa, amma ba su gajiya ba har Allah ya sa muka kai munzilin hankali.

Yaya aka yi ka samu kanka a matsayin ɗanjarida, marubucin waƙoƙin Hausa, kuma marubucin adabi?

Sha’awa ce ta sa na shiga aikin jarida. Lokacin ina ƙarami, mahaifinmu ma’abocin sauraron radiyo da kuma kallon talabijin ne. Yau da gobe ina zama tare da shi ban farga ba sai na ji ina so nima wata rana a dinga ji na a rediyo ko a kalle ni a talabijin. 

Batun adabi kuwa, kasancewata ɗalibin adabin Turanci (Literature in English) a makarantar sakandire ya ƙarfafa ni sosai wajen ƙara ƙaimi wajen karance-karance da bibiyar wuraren da ake harkokin da suka shafi adabi. Da rubutun wasan kwaikwayo na fara, saboda ina ganin ya fi sauƙi. Rubuta rahotanni da sharhin bayan labarai a aikin jarida ya sa na fara jin shi ma rubutun zuben zan iya. Amma an ɗauki lokaci mai tsawo ina saƙe-saƙe ban rubuta ko da gajeren labari ba. Kawai sai Allah ya kawo lokacin Korona, abin da ya sauya komai game da sha’awar da nake yi wa adabi.

Kasancewata ɗalibi a Kwalejin Marubuta Hausa da ke karatu onlayin ya ba ni damar ƙara ilimi da kuma haɗuwa da ma’abota adabin Hausa daban-daban. A wannan kwalejin ce aka fara wallafa gajeren labarin da na rubuta mai take ‘Tsananin Rabo’ a wani kundin littafi da ya ƙunshi gajerun labarai na ɗaliban kwalejin na wancan lokacin, mai suna ‘Dukan Ruwa Ba Ya Hana Gwarje Amo’, wanda Malam Kabiru Yusuf Fagge da Ibrahim Muhammad Indabawa suka yi aikin tacewa da tattara su waje guda. 

A daidai wannan lokacin kuma, na fara karatun digiri na biyu a harshen Hausa a Buɗaɗɗiyar Jami’ar ƙasa ta National Open University wacce ta buɗe Sashen Nazarin Harsuna, har da Hausa a ciki.

Za ka iya tuna lokacin da ka fara rubuta waƙoƙin hikima da gajerun labarai? Wanne ka fara yi a cikinsu?

A lokacin zaman gida na kullen Korona ne na fara rubutun waƙoƙi ina sa wa a shafina na facebook. Wasan kwaikwayo da gajerun labarai na fara rubutawa amma daga baya na fi mayar da hankali kan rubutattun waƙoƙi, abin da a baya nake yi wa kallon mai wahala sosai.

Wacce alaƙa aikin da ka ke yi na koyarwa yake da shi da ayyukan da ka ke yi na ƙirƙira da hikimomi?

Aikin koyarwa yana da alaƙa sosai da aikin ƙirƙira da hikimomi. Alaƙa ta farko dukkansu ayyuka ne na bincike da zurfafa tunani. Yadda malami a kullum yake bincike domin ya ƙaro ilimi, haka shi ma marubuci. Haka kuma, yadda malami ke mu’amala da ɗalibai masu halaye da dabi’u mabambanta, haka shi ma marubuci ke yi da sauran mutanen gari.

Kawo yanzu ka rubuta labarai da waƙoƙi sun kai nawa? Kawo sunayen wasu daga ciki da jigogin da suka ƙunsa.

Kawo yanzu na rubuta labarai guda uku. Na farko shi ne, ‘Tsananin Rabo’ wanda gajeren labari ne. Sai kuma littafin da na wallafa na farko wanda na sa wa suna, ‘Yi Wa Wani Yi Wa Kai.’ Akwai kuma wani gajeren labarin da na rubuta mai taken, ‘Amaryar Nuhu’. Akasari labaran suna bayani ne kan ƙalubalen tsaro da muhimmancin neman ilimi da kuma tsaftar muhalli.

Waƙoƙi kuwa ban san adadinsu ba saboda don haka kawai lokaci zuwa lokaci nake jin buƙatar rubuta su. Amma ina so na tattara waɗanda na iya samu na mayar da su littafi nan gaba da yardar Allah, kamar yadda wani abokina ya ba ni shawara tunda farko.

Jigogin rubutattun waƙoƙina sun haɗa da sanin ciwon kai, ilimi, kula da lafiya, tsaftar muhalli da jiki, tsaro, shugabanci nagari, dogaro da kai, taimakon juna da sauransu.

Bani labarin yadda aka yi ka fara tunanin wallafa littafin ‘Yi Wa Wani’ da ka fitar? Shi ne na farko ko akwai wasu kafin shi?

Tun lokacin da na fara rubuta littafin kusan shekara biyar baya na sa a raina cewa watarana zan wallafa shi da yardar Allah. Shi ne kuma ya kasance littafina na farko. Sai dai kuma kawo yanzu ba zan iya cewa komai game da karɓuwarsa ba, domin bai daɗe da fitowa ba.

Yaya ka ke ganin tasirin fasahar zamani wajen ragewa mutane shauƙin son karatun littafi?

Fasahar zamani ta yi tasiri sosai wajen rage karatun littafi, ba litattafan Hausa ba kaɗai. Kasantuwar galibin littattafai yanzu ana fara wallafa su a onlayin, ba kasafai za ka ga mutane na hulɗa da littafi na zahiri kamar yadda ake yi a baya ba.

Shin kana tunanin nan gaba za ka sake buga wani littafin?

In sha Allahu, da yardar Allah ina da burin buga wani littafin a ɓangaren adabi nan gaba. 

Kana cikin ɗaliban farko na Kwalejin Marubutan Hausa da aka taɓa buɗewa a manhajar WhatsApp, domin horar da matasan marubuta, yaya ka ga tasirin wannan makaranta, da cigaban da yanzu ake samu a harkar rubutun Adabi?

Kwalejin Marubutan Hausa ta yi tasiri a kaina sosai. Kuma na san su ma sauran ɗalibanta sun tasirantu da ita. Kwalejin ta koya mana muhimman abubuwa da ya kamata marubuci ya yi la’akari da su wajen tsara labari. A kwalejin na san matakan da ake bi wajen wallafa littafi har ma da kasuwancinsa.

Akwai wani ƙarfafa gwiwa da za ka yi wa marubuta maza kan dawo da rubutun da suke yi a baya, a maimakon bar wa marubuta mata su ci karensu babu babbabaka?

Ina fata yanayin da ya ja hankalin maza suka duƙufa wajen rubuce-rubuce a baya, zai dawo nan gaba. Al’adar karance-karance, musamman na littafi, tsakanin ɗalibai, da ma sauran mutanen gari, ta yi rauni sosai. Kuma wannan matsala za ta kau ne idan masu ruwa da tsaki a harkar ilimi suka haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen daidaita lamarin.

Wanne buri ka ke da shi nan gaba a fagen rubuce-rubuce?

Burina kan rubuce rubuce nan gaba shi ne na rubuta littafin da zai yi tasiri ga rayuwar mutane.

Wacce alaƙa ce ke tsakanin rubutun adabi da aikin jarida?

Alaƙar da ke tsakanin rubutun adabi da aikin jarida alaƙa ce irin ta ɗanjuma da ɗanjummai. Wato duk su biyun ayyuka ne da ke da alaƙa da faɗakarwa da ilimantarwa da kuma nishaɗantarwa tsakanin al’umma. Sannan kuma dukkansu sana’o’i ne masu daraja idan an yi su yadda ya kamata.

A duk lokacin da ka keɓe kana hutawa, wanne abin nishaɗi ne ya fi ɗaukar hankalinka?

Ni mutum ne mai sha’awar buga ƙwallo sosai. Don haka a duk lokacin da na ji dugudugu, nakan so na ɗan fita domin na tsinka jini.

Kana samun damar karanta littafin wasu marubutan Hausa kuwa? Wanne ne littafin ne ka ke karantawa a yanzu?

Nakan karanta littattafan Hausa na da da na yanzu a duk lokacin da na samu dama.  A halin yanzu babu wani littafi da nake karantawa.

Gaya mana karin maganar da ya fi tasiri a rayuwarka?

Karin magana mafi tasiri a rayuwata shi ne “Alheri danƙo ne, ba ya faɗuwa ƙasa banza”.

Madallah, mun gode.

Alhamdulillah. Ni ma na gode sosai.

By ukarofi