
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Real Madrid da Hukumar Kula da Ƙwallon Ƙafa ta Turai (UEFA) sun sanar da cimma yarjejeniya domin kawo ƙarshen rikicin sharri’o’i da ya biyo bayan rushewar gasar European Super League.
Madrid, wadda shugabanta Florentino Perez ya daɗe yana goyon bayan gasar, tare da kamfanin A22 Sports Management, sun sanar da kawo ƙarshen shirin gasar European Super League a hukumance bayan an cimma yarjejeniya tsakanin UEFA, Kungiyoyin Kwallon Kafa na Turai (EFC), da kuma Real Madrid.
An kirkiro tunanin Super League ne shekaru biyar da suka gabata tare da kungiyoyi kamar Real Madrid, Barcelona, Atlético Madrid, AC Milan, Arsenal, Chelsea, Inter Milan, Juventus, Liverpool, Manchester City, Manchester United, da Tottenham a matsayin kungiyoyin kafa ta.
Saidai a tsawon lokaci, Florentino Pérez ya rage shi kaɗai a wannan yunkuri, kuma daga karshe ba shi da wani zaɓi face kawo ƙarshen wani shiri da bai taɓa fara aiki yadda ya kamata ba.
