An kama matashiya ‘yar 18 da zargin kai hari wata makaranta a Kanada 

Spread the love

Jami’an ‘yan sanda a Kanada sun bayyana cewa, wata matashiya mai shekaru 18, Jesse Van Rootselaar, ce ta kai harin bindiga a wata makaranta a yankin British Columbia, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane tara ciki har da ita kanta.

Da farko an ruwaito mutuwar mutum goma, amma daga bisani aka gyara adadin zuwa tara. Lamarin ya faru ne a wata ƙaramar alƙarya mai mutane kusan 2,400 a Tumbler Ridge.

‘Yan sanda sun ce ana zargin ta fara kashe mahaifiyarta mai shekaru 39 da kuma ɗan uwanta ɗan shekara 11 a gida kafin ta nufi tsohuwar makarantar da ta taɓa karatu a can.

An ce ta taɓa shiga hannun hukuma sau da dama ƙarƙashin dokar kula da lafiyar kwakwalwa ta lardin. Bayan kai harin, ta kashe kanta.

Ta harbe wata malama mai shekaru 39, ɗalibai mata uku masu shekaru 12, da ɗalibai maza biyu masu shekaru 12 da 13. An samu bindiga mai tsawo da kuma ƙaramar bindiga da aka gyara a wurin.

Firaministan Kanada, Mark Carney, cikin alhini ya bayyana cewa, ƙasar na cikin jimami. An sauke tutoci rabin-kasa na tsawon kwanaki bakwai.

Kanada ba kasafai ake samun hare-haren makaranta ba kamar Amurka, lamarin da ya sa wannan harin ya girgiza al’umma matuƙa. Duk da cewa dokokin mallakar makami a Kanada sun fi tsauri, an bayyana cewa wadda ake zargi ta taɓa mallakar lasisin bindiga wanda ya ƙare a 2024.

Wannan hari ya shiga sahun hari mafi muni a tarihin ƙasar, tare da sake tayar da muhawara kan lafiyar hankali da dokokin makami.

By ukarofi