
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Asabar Shugaba Bola Tinubu ya bayyana taron Bajekolin Kamun Kifi da Al’adu na Argungu karo na 61 a matsayin yanayin da ke nuna al’amura a Jihar da ma Nijeriya baki ɗaya sun dawo daidai.
Da yake jawabi a taron wanda aka yi a Argungu, Shugaban Ƙasar ya ci alwashin Gwamnatin Tarayya za ta cigaba da bayar da tallafi ga harkokin walwalar al’umma, noma, tsaron abinci da kuma inganta yankunan karkara.
Ya kuma yaba wa gwamnatin jihar Kebbi bisa shirya taron mai daɗaɗɗen tarihi da ya haɗa aƙalla masunta 50,000 daga sassa Nijeriya.
Taron, wanda aka yi na kwana huɗu, ya ƙunshi watannin al’adu, gasar iyo, dambe da kuma rawa, inda shugaban ya kuma jinjinawa jami’an tsaro bisa kimstinsu wajen ganin an gudanar da taron cikin aminci.
Kazalika, bayan isar sa, Tinubu ya ƙaddamar da wasu manyan ayukka da suka haɗa da: Sabon ginin sakatariyar gwamnatin jihar Kebbi, titin Sarki Haruna mai falle uku a Birnin Kebbi, Kwalejin Ungozomanci ta Ambursa, babbar tashar mota ta jihar Kebbi da kuma titin Argungu By-Pass da aka faɗaɗa.

