Gwamnan Kano ya tsige na hannun daman Kwankwaso, Buba Galadima a shugabancin majalisar gudanarwar Polytechnic

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sallami Injiniya Buba Galadima, wato babban na hannun Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso daga muƙamin shugaban hukumar gudanarwar makarantar Polytechnic ta Kano.

Buba Galadima ya shiga sahun waɗanda suke sukar gwamnan tun daga lokacin da ya (Abban) fice daga tafiyar Kwankwasiyya.

Kakakin Gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanar da haka ta wata sanarwa a jiya Asabar.

A cewar sanarwar, Abba ya kuma amince da naɗin Sarkin Gaya, Alhaji Dakta Aliyu Ibrahim Abdulkadir a matsayin wanda zai maye gurbin Galadima a muƙamin.

Ta bayyana cewa an ɗauki matakin tsige Galadima ne bisa yunƙurin da gwamnatin jihar ke yi wajen sauye-sauyen daidaita lamuran makarantar da tsarin gwamnatin na Kano First Agenda.

Duk da cewa naɗin na wa’adi shekaru uku ne, an tsige Buba Galadima gabanin cikar lokacin saboda tsarin gyare-gyaren.

Gwamnan ya kuma yi godiya ga Galadima bisa guddumuwar da ya bayar a lokacin da yake riƙe da ofishin.

Kazalika, Abba ya kirayi sabon wanda aka naɗa a muƙamin da ya yi amfani da ƙwarewarsa da kwarjinin jagorancinsa wajen daidaita al’amuran makarantar

By Babaji