Gwarzon bikin kamun kifin Argungu ya samu kyautar miliyan N1 da motoci

Spread the love

Abubakar Usman daga ƙaramar hukumar Maiyama ta Jihar Kebbi ne ya lashe gasar kamun kifin Arugungu ta 2026.

Kifin da ya kama na da nauyin kilogiram 59, kamar yadda alƙalan gasar suka sanar lamarinda ya ba shi damar zama gwarzon gasar.

Abubakar ya samu kyautar motoci guda biyu ƙirar Toyota da kuma Naira miliyan ɗaya.

Dubban masunta ne suka shigar gasar kamun kifin, wadda aka jima ana yi, inda wannan ta zama ta 61.

ShugabaBola Tinubu ne babban baƙon da ya halarci gasar, inda dubban mutane daga ciki da wajen Nijeriya suka halarta.

By Babaji