WAIWAYE: Yadda INEC ta ɗage zaɓen 2003 bayan Kiristoci sun yi zanga-zangar haɗewarsa da Easter

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Zaɓe Mai zaman kanta ta Ƙasa INEC, ta ɗage babban zaɓen da aka yi a shekarar 2003 bayan Kiristoci sun gudanar da zanga-zanga akan haɗewarsa da lokacin bikin Easter.

Da fari an sanya 19 ga watan Afrilu, 2003 a matsayin lokacin zaɓen gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi, wanda hakan ya yi kiciɓis da Asabar Mai Girma, wato ‘Holy Saturday’ ta gabanin ‘Easter Sunday, wanda muhimmin lokaci ne a kalandar Kiristoci.

Akan haka jama’ar suka tayar da hazo, inda suak yi gargaɗin cewa yin zaɓe a lokaci mai muhimmanci irin wannan zai hana Kiristoci da dama yin zaɓe.

Kuma a lokacin, musamman ƙungiyar Catholic Bishops’ Conference of Nigeria (CBCN) ta bayyana ƙin amincewar ta ƙarara, inda ta buƙaci hukumar zaɓen da ta sake nazari.

Ta kuma nemi INEC da sauya lokacin zaɓen ta yadda za a bai wa ɓangarorin al’ummar damar shiga a dama da su da tabbatar da haɗin kan ƙasa.

Zanga-zanga ta janyo cece-kuce musamman akan buƙatar samar da daidaito a harkokin lokutan zaɓe bisa la’akari da hidindimun addini.

Daga nan ne INEC ta sauya lokacin zaɓen gwamnonin zuwa wani lokaci acikin watan.

By Babaji