
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya aike wa Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara Akan Harkar Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu saƙo cewa ya fayyace batun da ke zargin ofishinsa (ONSA) da sayo sinadarin ‘thallium sulphate’, wadda guba ce mai matuƙar haɗarin gaske.
El-Rufai ya bayyana hakan ne a yau Lahadi acikin wani saƙo da ya wallafa a shafin sa na X, inda ya haɗa kwafin wasiƙar da ya aike wa ONSA a Abuja.
Ya ce, “A matsayin na ɗan ƙasa, na rubuta wa NSA domin neman ƙarin haske kan rahotannin da ke cewa ofishin sa ya shigo da thallium sulphate, wata guba mai matuƙar haɗari. Abu ne mai tayar da hankali idan wani ya shigo da kowace irin guba, musamman wadda ba ta da ƙamshi ko launi.”
El-Rufai ya ce, bayanan da ke hannun shugabannin ’yan adawa sun nuna cewa ONSA ta sayo kimanin kilo 10 na thallium sulphate daga wani kamfani a ƙasar Poland.
Ya bayyana gishirin thallium a matsayin sinadari mai tsananin guba wanda ake takaita sarrafawa a kansa, yana mai cewa tsaron jama’a, alhakin dimokuraɗiyya da amincewa da cibiyoyin ƙasa na buƙatar a yi gaggawar yin bayani.
Ya buƙaci a bayyana manufar amfani da sinadarin, sunan kamfanin da ya samar da shi, da ko an shigo da shi ne da sahalewar da ta dace a ƙarƙashin dokokin sinadarai ko na tsaro.
Kazalika, ya nemi a fayyace adadin da aka shigo da shi, irin sa ko ƙarfin sa, da yadda aka adana shi da matakan tsaron da aka ɗauka bayan isowarsa.
Bugu da ƙari, ya tambayi irin sa-ido da haɗin gwiwar da aka yi da Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna (NAFDAC) da Cibiyar Kula da Yaɗuwar Cutuka ta Ƙasa (NCDC), da kuma ko an tantance haɗarin lafiyar jama’a ko shirye-shiryen rage matakin illarsa acikin al’umma.
