
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya kasance a halin bincike har zuwa daren Litinin wayewar Talata a komar Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) a Abuja, sa’o’i bayan amsa gayyatarta ta zargin sa da hannu a badaƙalar Naira biliyan 432.
Majiyoyi da dama daga hukumar sun ce, El-Rufa’i, wanda ya je ofishin tun ƙarfe 10 na safe, ya kai har cikin dare a komar hukumar ana gudanar da bincike akansa.
Tsohon gwamnan, wanda a yanzu jigo ne a jam’iyyar ADC, ana tuhumar gwamnatinsa ne da sauya akalar kuɗaɗen da aka ciyo bashinsu, saɓa wa ƙa’idojin bayar da kwangiloli, wanda hakan ya jefa jihar cikin matsanancin bashi daga shekarar 2015 zuwa 2023, kamar yadda majalisar dokokin jihar ta bayyana a shekarar da ta gabata.
An fara binciken El-Rufa’i ne bisa la’akari da abin da ƙwarya-ƙwayar kwamitin majalisar ya gano akan lamuran kuɗaɗen jihar.
Kakakin majalisar, Yusuf Ɗahiru Leman ya shaida wa ‘yan majalisar cewa jimillar biliyan N432 ne aka zuƙe, lamarin day a jefa jihar Kaduna cikin halin ni-‘yasu na matsanancin bashi.
Akan haka ne kwamitin ya nemi a gurfanar da tsohon gwamnan da manyan jami’an gwamnatisa bisa zargin su da saɓa wa dokokin aiki, rashin bin doka wajen bayar da kwangiloli, almundahanar kuɗaɗe, karɓo basussuka mara misali da sauya akalar dukiyar al’umma.
Daga cikin zarge-zargen akwai biyan wasu kuɗaɗe da ake da rikici akansu da kwangiloli da adadinsu ya kai jimillar sama da miliyan N155, zargin sauya akalar biliyan 1.37 na aikin titin jirgin ƙasa da sace miliyan N64.8 daga ɓangaren manyan jami’ai.
