Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Rahotanni sun nuna cewa rundunar sojojin Nijeriya ta sake kama wasu mutane bisa zargin hannu a wani sabon shiri na kifar da gwamnatin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
A cewar Sahara Reporters, daga cikin waɗanda aka tsare har da Manjo H. Yusuf na rundunar sojojin ƙasa, wanda ya kammala kwas na manyan jami’ai a Kwalejin Horas da Hafsoshin Soji da ke Jaji. Ana tsare da shi tare da wasu da ake zargi da hannu a yunƙurin juyin mulki, kodayake har yanzu hukumomi ba su fito da cikakken bayani kan zargin ba.
Bincike kan lamarin ya fara tun shekarar 2025, amma kawo yanzu ba a fara shari’a a hukumance ba, kuma bayanai kan yadda ake zargin shirin ya gudana sun kasance cikin duhu.
Masu sa ido kan harkokin tsaro sun bayyana yanayin a matsayin mai cike da ruɗani, sakamakon ƙarancin bayanan da ake fitarwa.
Rahotanni sun nuna cewa, an fara kitsa shirin ne tun lokacin miƙa mulki daga tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari zuwa Shugaba Bola Tinubu a ranar 29 ga Mayu, 2023, amma aka dakatar da shi saboda rashin isassun kuɗi da shirye-shiryen dabaru. Ana zargin cewa an sake farfaɗo da shirin a 2025 bayan tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Timipre Sylva, ya tura kusan naira biliyan ɗaya ta asusun banki daban-daban zuwa hannun wani ɗan canji.
Har ila yau, ana zargin wani tsohon babban jami’in soja mai ritaya, Manjo Janar Adamu, da kasancewa cikin manyan masu tallafa wa shirin. Rahotanni sun ce shi da wasu uku har yanzu suna can a waje.
Da fari, an kama jami’an soja aƙalla 16 da ake zargi da hannu kai tsaye. Sai dai daga bisani, bayan kafa kwamitin bincike na musamman ƙarƙashin jagorancin Babban Hafsan Leƙen Asirin Soji, Manjo Janar Emmanuel Undiandeye, adadin waɗanda aka kama ya ƙaru zuwa 40, ciki har da manyan jami’ai daga sassa daban-daban na rundunar soji.
Wasu daga cikin waɗanda aka ambata sun haɗa da Birgediya Janar MA Sadiƙ, Kanar MA Ma’aji, Laftanar Kanar S Bappah da wasu jami’an bataliyoyi da rundunonin musamman. Rahotanni sun kuma ce akwai fararen hula a cikin waɗanda ake zargi, ciki har da ma’aikatan fadar gwamnati da wani jarumin fina-finai da ake zargin an ɗauke shi domin yaɗa farfaganda.
Ana kuma zargin cewa masu shirin juyin mulkin sun sanya manyan jami’an gwamnati cikin jerin waɗanda suke son kai wa hari, ciki har da Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, da Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, tare da manyan hafsoshin tsaro.
Yayin da gwamnati da rundunar soji ba su fitar da cikakken bayani ba, lamarin na ci gaba da janyo muhawara a faɗin ƙasa kan haƙiƙanin abin da ke faruwa a bayan fage da kuma tasirin sa ga tsaron dimokuraɗiyyar Nijeriya.
