Gwamnatin Kano ta fara duba tsarin ciyar da masu azumi a watan Ramadan

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta fara rangadin duba yadda ake shirya da rarraba abinci ga masu azumi a faɗin jihar a cikin watan Ramadan mai alfarma.

Rangadin na da nufin tabbatar da cewa ana gudanar da shirin ciyarwar cikin tsari, tare da kiyaye tsafta da bin ƙa’idojin da gwamnati ta gindaya domin amfanin al’umma.

Shugaban kwamitin kuma kwamishinan harkokin Addini, Sheikh Tijjani Auwal Sani, ne ya jagoranci tawagar yayin ziyarar da suka kai cibiyoyi daban-daban na rabon abincin.

Ya bayyana cewa gwamnati ta ƙaddamar da wannan duba ne domin tabbatar da cewa masu azumi suna samun ingantaccen abinci wanda aka tanada cikin tsafta, tare da rarrabawa cikin adalci a duk wuraren da aka ware.

A yayin rangadin, kwamitin ya kai ziyara cibiyoyi da dama, ciki har da Masallacin Sheikh Tijjani Bala Kalarawi da ke ƙaramar hukumar Fagge, da kuma Asibitin Hasiya Bayero da ke ƙaramar hukumar Municipal.

A wuraren, sun duba yadda ake sarrafa abinci, yanayin tsafta, da kuma yadda ake rarraba shi ga masu cin gajiyar shirin.

Kwamitin ya kuma tattauna da jami’an da ke kula da shirin domin jin ƙalubalen da suke fuskanta tare da nemo hanyoyin inganta aiki.

Sheikh Tijjani Auwal Sani ya yaba da ƙoƙarin masu gudanar da shirin, yana mai jaddada cewa gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ba za ta lamunci sakaci ko saɓa ƙa’idojin da aka shimfiɗa ba.

Ya ƙara da cewa shirin na da matuƙar muhimmanci wajen tallafawa masu azumi, musamman marasa ƙarfi, a wannan wata mai albarka.

A ƙarshe, shugaban kwamitin ya tabbatar da cewa za a ci gaba da gudanar da wannan rangadi a faɗin jihar domin tabbatar da ingancin shirin.

Haka kuma ya buƙaci al’umma da su ba gwamnati haɗin kai tare da kai rahoton duk wata matsala domin tabbatar da cewa abincin na kai wa ga waɗanda aka tanada domin su.

By ukarofi