2026: Nasarori da akasin bikin kamun kifin Argungu

Spread the love

*Yadda bikin ya zama na musamman a Afrika

*An rasa rayukan mutum biyu

*An sace fitilun da aka saka jim kaɗan bayan kammala bikin

*An yi ƙorafi kan tsafta da kwamitoci

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi

Biki nan mai cike da tarihi da ƙayatarwa a Afrika na kamun kifi a Argungu, wanda ake gudanarwa shekara-shekara, yana ɗaya daga cikin bukukuwan nuna al’adun gargajiya da ake yi a garin Argungu da yake a Jihar Kebbi, inda nan ne cibiyar Daular Muhammadu Kanta, wanda yana ɗaya daga cikin gwamnonin Muhamma Askia na Masarautar Songhai a baya.

Bikin kamun kifi na Argungu ya samo asali ne a wata ziyarar kawo wa ƙarshen yaƙe-yaƙe da aka yi tsakanin Masarautar Sokoto da kuma wannan yankin na Kabi da Sarkin Musulmi Hassan Hassan ɗan Mu’azu ya yi a shekara ta 1934, inda aka shirya wasannin gargajiya daban-daban. Daga baya sai masarautar Kabi ta yanke shawarar a yi gangamin kamun kifi, don tarben babban baƙo.

Wannan gagarumin gangamin ya burge Sarkin Musulmi Hassan ɗan Mu’azu, wanda daga ƙarshe ya yi addu’ar ɗaukaka ga wannan al’amarin.

Daga wannan lokacin masarautar Kabin Argungu ta mayar da shi bikin shekara-shekara tare da ƙara waɗansu al’adun gargajiya da suka haɗa da nunin amfanin gona da kokawa da dambe da gasar harbin kibiya da gasar hawan doki, jakuna da raƙuma da nuna hikimomin Kabawa kamar lalabe, shako, tseren iyo, hawan kyarta, hawan giginya da tseren kwale-kwale da tseren keke da dai sauransu.

Aƙalla wannan kogin na Matan Fada, inda a ke gudanar kamun kifin, mutane dudu biyu kan iya shiga lokaci ɗaya kuma kowa zai sami kifi iya sa’arsa, waɗansu sukan kama manya, waɗansu kuma sukan kama ƙanana, inda a ke bai wa wanda ya kama kifi mafi girma kujerar hajji da lambar yabo da kyautuka daban-daban. Na biyu har zuwa na 50 ma akan ba su kyautuka daban-daban. Sai dai a bana (shekara ta 2026) har zuwa na 100 duk za su sami kyautuka.

Da ya ke bikin an daɗe ana aiwatar da shi ne a ƙarƙashin masarautar Kabin Argungu, sai kuma daga baya gwamnatin jiha, tun ana Jihar Sokoto, ta karɓa, inda bayan ƙirƙiro Jihar Kebbi a shekarar 1991, bikin ya dawo ƙarƙashin kulawar Jihar Kebbi. 

Bisa ga nasarorin da ake ta samu a wannan bikin, Mai Martaba Sarkin Kabi, Alhaji Sama’ila Muhammad Mera, ya shiga ya fita har bikin yanzu yana ƙarƙashin Gwamnatin Tarayya, wanda yin haka ya ƙara wa bikin armashi da ɗaukaka.

Bikin kamun kifin ya janyo wa garin Argungu da Jihar Kebbi suna a idon duniya, saboda baƙi daga ciki da wajen Nijeriya sukan halarci wannan taron a duk lokacin da aka fitar da sanarwar bikin, domin su saka hannun jari.

Daga cikin wuraren da baƙi ke ziyara akwai gidan tarihin Kanta da ake kira Gidan Nabame, inda aka ajiye kayan da aka yi yaƙi da su tun lokacin Muhammadu Kanta da kuma wuraren da aka rufe sarakunan wannan masarautar ta Kabin Argungu.

Bikin ya shekara 92 da fara shi kenan a wannan shekara ta 2026, inda Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya samu halarta da kansa, kuma aka kama kifi mafi girma mai nauyin kilogiram 59.

Ba shakka masarautar Kabin Argungu a ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammad Mera da Gwamnatin Jihar Kebbi da ta Tarayya sun shirya wa bikin kamun kifi na wannan shekarar ta 2026, saboda an ɗauki matakin samun nasarori ta kowane ɓangaren tun kama daga samar da tsaro shirya masaukan baƙi, tsaftace gari da yaɗa sanarwa, musamman ga masunta, wanda shine babban abinda ake son shugabanni su gani ta hanyar kafafen yaɗa labarai daban-daban.

An sami nasara wajen gasa daban-daban tun daga rana ta farko da aka soma tseren raƙuma da jakuna da harbin kibiya da harbin danƙo duk da ya ke dai ba a sami wanda ya sami maki ɗari bisa ɗari ba.

Haka zalika a rana ta biyu da a ke nuna amfanin gona da fiɗar awaki da jayayya tsakanin Kabawa (masu sana’arsu) da Rundawa (’yan fawa) da kuma naɗin Sarkin noman shekara da dai sauransu. Sai kuma da yamma an gudanar da wasan dambe da kokawa, yayin da a ranar Juma’a aka gudanar da gasar tseren iyo na maza da mata da tseren kwale-kwale na maza da mata da kamun dumulmule (tsuntsun ruwa) da laluben kifi da hannu na maza da mata da kuma shaƙo (nutso). Dukkan waɗannan wasannin an gudanar da su kuma sun ƙayatar ainun.

Sai kuma a ranar Assabar  ne ake kamun kifi a kogin Matan Fada, wanda an sami halartar mutane daga ciki da wajen Jihar Kebbi, inda a wannan shekarar aƙalla sama da mutane dubu hamsin ne suka shiga wannan gasar ta kama kifin da ya fi dacewa kowanne nauyi.

A bana dai an sami kifi mai  nauyin kilogiram 59, wanda Usman Abubakar, ɗan asalin ƙaramar Hukumar Maiyama ya kamo, inda ya sami kyautar Naira miliyan ɗaya da kujerar hajji da motoci biyu da sauran kyautuka daga mutane daban-daban.

Sai dai a ɗaya ɓangaren kuma an sami asarar rayuka biyu a wajen gasar shaƙo (nutso) bayan da mutane uku suka yi saura a nutse cikin ruwa har na tsawon mintuna bakwai da waɗansu daƙiƙoƙi aka lalubo su, yayin da ɗayan ya rasu nan take, aka garzaya da ɗaya a asibiti inda daga baya ya rasu.

A ɓangaren Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kebbi ba shakka sun yi ƙoƙari wajen fitar da maƙudan kuɗaɗe, don gyare-gyaren wuraren da baƙi za su yi amfani da su da kuma tsaftace gari.

Sai dai a nan kam an sami akasi, don baƙi, musamman ’yan jarida da suka zo daga kafafen yaɗa labarai, sun koka bisa ga rashin masauki mai tsafta. ɗakunan da aka bai wa ’yan jaridar babu ɗaya da aka kammala gyaran sa, saboda babu wuta, babu ruwa, babu banɗaki yayin da waɗansu ɗakunan babu ko daɓen ƙasa. Haka zalika a cikin garin Argungu har hanyoyin da a ke bi a lokacin hawan daba ba a kwashe shara ba.

Malam Aliyu Ibrahim Argungu ya bayyana wa Wakilin Blueprint Manhaja da cewa, gaskiya ’yan kwamitocin da aka danƙa wa amana, ba su kyauta ba, saboda an ce an bai wa kwamitocin kuɗaɗe, don aiwatar da waɗannan ayyukan, amma babu abinda suka yi.

Ya nemi Gwamna Malam Nasir na jihar ta Kebbi da kuma Masarautar Kabin Argungu su nemi ba’asi daga kwamitocin da aka naɗa kuma duk wanda aka kama da laifi a hukunta shi ko kuma ya mayar da kuɗaɗen da ya karɓa.

Wani daga cikin ’yan kwamitocin da bai so a bayyana sunansa ba, ya bayyana wa Wakilin Blueprint Manhaja da cewa, shi an dai kira shi an ce yana ɗaya daga cikin ’yan kwamitin ɗaya daga cikin abubuwan da za a yi a bikin kamun kifi na wannan shekarar, amma tun daga wannan lokacin ba a sake kiran sa ba sai ranar Litinin bayan kwanaki biyu da kammala bikin aka kira shi aka ba shi Naira 15,000 aka ce wai nasa ne na kwamitin. Ya ƙara da cewa, shi da kan sa bai gamsu da yadda aka yi waɗannan ayyukan ba, sai dai a tunaninsa, an siyasantar da lamarin ne kawai.

Haka-zalika bayan kammala bikin kamun kifin, duk wuraren da aka bayar da kwangilar saka fitilu masu amfani da hasken rana, saboda samar da tsaro ko bayan bikin musamman filin Suka, inda waɗansu ɓata-gari ke aikata baɗala da daddare, ana zargin waɗannan mutanen sun je sun cire su sun sayar, duk da yake an bayar da kwangilar ne da zummar harbin tsuntsu biyu da dutse ɗaya, ta yadda bayan kammala bikin zai amfani al’ummar Argungu. Don haka ake ganin ya kamata masarautar Kabin Argungu ta saka baki, don a mayar da waɗannan kayan hasken rana.

ƙoƙarin da Wakilin Blueprint Manhaja ya yi na jin ta bakin ’yan kwamitin ko jami’an tsaro ya ci tura. Haka nan kawo yanzu gwamnatin jiha ko ta tarayya ba su fitar da wata sanarwa kan hakan ba har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto.

By ukarofi