Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Leƙen Asiri ta Soji (DIA) ta miƙa Malamin addinin Musulunci, Sheikh Sani Abdulkadir Zariya, hannun Hukumar Farin Kaya (DSS), domin ci gaba da bincike kan zarginsa da hannun a ƙoƙarin yin juyin mulki a Nijeriya.
An kama malamin ne saboda zarginsa da hannu wajen yunƙurin kifar da gwamnatin Bola Tinubu.
A baya, wani alƙalin Kotun Tarayya da ke Abuja, ya umarci DIA da ta kawo malamin kotu a ranar 18 ga watan Fabrairu domin duba yiwuwar bayar da belinsa.
Amma a lokacin sauraron shari’ar, lauyansa ya shaida wa kotu cewa DIA ba ta kawo shi ba saboda ta riga ta miƙa shi hannun DSS.
Malamin ya kuma shigar da ƙara don neman a saki shi.
Malamin ya yi ƙarar EFCC, DIA, Lauyan Gwamnati, da kuma bankin Jaiz.
Iyalinsa sun ce kama shi da aka yi ba zai rasa nasaba da kyautar miliyan biyu da aka tura wani malami wanda ake bincike a kansa kan zargin a hannu a yunƙurin juyin mulki.
Alƙalin ya ce an tsare malamin ne tun ranar 11 ga watan Disamba, 2025, saboda dalilai na tsaro.
