Tinubu ya nemi gwanjon jiragen Jamus don ƙarfafa tsaro

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya roƙi gwamnatin Jamus da ta miƙa wa Nijeriya wasu tsofaffin jiragen sama masu saukar ungulu domin ƙarfafa ayyukan leƙen asiri da sa ido a yankin Sahel, wanda ke fama da matsalar tsaro.

Shugaban ya bayyana buƙatar ne yayin wata tattaunawa ta waya da Kansilan Jamus, Friedrich Merz, a yammacin ranar Laraba, tattaunawar da ta ɗauki kusan mintuna goma.

A cewar mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, shugabannin biyu sun amince da zurfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, tare da ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa a ɓangarorin tsaro, lantarki da layin dogo.

Tinubu ya jaddada cewa yankin Sahel na buƙatar tallafin haɗin gwiwa daga ƙasashen duniya, musamman ta fuskar leƙen asiri da sa ido daga sama, domin daƙile barazanar ta’addanci da ke yaɗuwa a yankin. Sai dai sanarwar ba ta bayyana ko gwamnatin Jamus ta amince da buƙatar miƙa jiragen saman ba.

Baya ga batun tsaro, shugabannin sun tattauna kan shirin inganta wutar lantarki da ake aiwatarwa tare da kamfanin Siemens, wanda ya kai kimanin dala biliyan 2.3. Shirin, wanda aka ƙaddamar tun 2019, ya fuskanci tsaiko duk da amincewar Majalisar Zartarwa ta Tarayya kan kashe maƙudan kuɗaɗe domin matakin farko na gyarawa da faɗaɗa layin wutar lantarki na ƙasa.

Tinubu ya bayyana cewa Nijeriya na buƙatar taimako a ɓangaren isar da wutar lantarki, inda Merz ya nuna aniyar cewa Siemens za ta ba da gudunmawa, yayin da Bankin Deutsche ke shirin taimakawa wajen samar da kuɗin aiwatar da aikin.

Har ila yau, an tattauna haɗin gwiwa a ɓangaren al’adu, inda Kansilan Jamus ya buƙaci kafa Babban Gidan Tarihi na Fasahar Afirka, tare da bayyana cewa ƙasarsa na jiran isowar sabon jakadan Nijeriya a Jamus.

Masu lura da al’amura na cewa idan aka amince da buƙatar jiragen sama masu saukar ungulu, hakan zai taimaka matuƙa wajen ƙarfafa ayyukan tsaro a yankin Sahel. Haka kuma, idan aka farfaɗo da aikin Siemens yadda ya kamata, hakan na iya zama mafita ga matsalar wutar lantarki da ta daɗe tana addabar ’yan Nijeriya.

By ukarofi