Jigawa, Legas da Sakkwato ne kan gaba wajen rajistar zaɓe, inji INEC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC), ta sanar da ƙaruwar yawan sabbin masu rajistar katin zaɓe a zagaye na biyu na rajistar masu kaɗa ƙuri’a, inda sama da ’yan Nijeriya miliyan 1.2 suka kammala rajista zuwa ranar 13 ga Fabrairu, 2026.

A sabuwar sanarwar da hukumar ta fitar ta shafinta na ɗ, INEC ta bayyana cewa jimillar mutane 1,228,648 ne suka kammala rajista a ƙarƙashin Mataki na II, Mako na Shida. Wannan adadi ya ƙaru daga 884,737 da aka samu a ƙarshen Mako na Biyar, alamar cewa sha’awar rajistar zaɓe na ƙaruwa a faɗin ƙasa.

Daga cikin adadin da aka samu: Mutane 673,124 sun fara rajista ta hanyar cike fom ɗin farko a yanar gizo. Mutane 555,524 sun kammala rajista a cibiyoyin da aka tanada a zahiri.

ƙididdigar ta nuna cewa, jihar Jigawa ce ta fi kowa yawan sabbin rajista da mutane 98,698 (kashi 8.03). Jihar Legas na biye da 86,307. Jihar Sakkwato na da 77,004. Jihar Kano na da 71,990. INEC ta bayyana cewa, akwai Mata: 696,891 (kashi 57), Maza: 531,757 (kashi 43).

A ɓangaren shekaru, matasa masu tsakanin shekaru 18 zuwa 34 sun kai 848,066, wanda ya zama kashi 69.02 na jimillar rajistar. Haka kuma, mutane masu buƙata ta musamman (PWD) da suka yi rajista sun kai 19,414 a faɗin aasa.

Rajistar na ci gaba a duk faɗin Nijeriya, sai dai a Babban Birnin Tarayya Abuja, inda aka dakatar da ita bisa tanadin dokar zaɓe saboda zaɓukan ƙananan hukumomi da za a gudanar a ranar 21 ga Fabrairu, 2026.

Mataki na II na CVR ya fara ne a ranar 5 ga Janairu, 2026, kuma ana sa ran zai ci gaba har zuwa Afrilu 2026. Wannan mataki ya biyo bayan Mataki na I da aka gudanar daga Agusta zuwa Disamba 2025, wanda ya ƙara kimanin masu zaɓe miliyan 2.78 a kundin rajista.

ƙaruwar rajistar na nuna yadda ‘yan Nijeriya ke ƙara nuna sha’awa da himma wajen shiga harkokin dimokuraɗiyya, musamman matasa da mata da ke taka muhimmiyar rawa a tsarin siyasa.

By ukarofi