Majalisar Ribas ta dakatar da shirin tsige Fubara

Spread the love

Daga MAHDI MUSA NUHAMMAD

Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta dakatar da shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara da Mataimakiyarsa, Ngozi Odu daga muƙamansu, bayan tsoma bakin Shugaban ƙasa, Bola Tinubu.

An cimma wannan matsaya ne a zaman majalisar na ranar Alhamis, inda aka bayyana cewa za a dakatar da duk wani ci gaba kan batun har sai kotuna sun yanke hukunci kan ƙararrakin da ke gabansu, tare da kammala shawarwarin siyasa da ake yi.

A watan Janairu ne ‘yan majalisar suka fara yunƙurin tsige gwamnan da mataimakiyarsa bisa zargin “mummunan rashin ɗa’a a ofis” kamar yadda Sashe na 188 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya tanada.

A zaman majalisar da Kakakin Majalisa Martins Amaewhule ya jagoranta, Shugaban Masu Rinjin Yawaye, Major Jack, ya gabatar da takardar zarge-zarge guda bakwai kan gwamnan. Daga ciki akwai: Rushe ginin majalisar jiha, kashe kuɗi ba tare da tanadin kasafin kuɗi ba, riƙe kuɗaɗen Hukumar Ayyukan Majalisa, ƙin bin umarnin Kotun ƙoli kan ’yancin cin gashin kan majalisa ta fuskar kuɗi

Jimillar ‘yan majalisa 26 ne suka sanya hannu kan takardar, wadda aka shirya turawa gwamnan.

Haka zalika, Mataimakiyar Shugaban Masu Rinjin Yawaye, Linda Stewart, ta gabatar da nata zarge-zarge kan mataimakiyar gwamna, inda ta tuhume ta da kashe kuɗi ba bisa ƙa’ida ba, daƙile ayyukan majalisa, amincewa da kasafi ta hanyoyin da ba su dace ba da kuma riƙe albashi da alawus-alawus.

Yunƙurin tsige gwamnan ya fuskanci tangarɗa bayan Babban Alƙalin Jihar Ribas, Simeon Chibuzor-Amadi, ya ki naɗa kwamitin bincike na mutum bakwai kamar yadda doka ta tanada. Ya bayyana cewa akwai umarnin wucin gadi daga Babbar Kotun Jihar Ribas da ya hana ɗaukar wani mataki kan batun.

Alƙalin kotun, Florence A. Fiberesima, ta bayar da umarnin a ranar 16 ga Janairu 2026, inda ta hana Babban Alƙalin Jiha, Kakakin Majalisa da Magatakardar Majalisa ɗaukar wani sabon mataki kan tsige gwamnan da mataimakiyarsa, bayan sun shigar da ƙara suna ƙalubalantar halascin tsarin tsigewar.

Rikicin ya janyo martani daga ɓangarori daban-daban, ciki har da jam’iyyar APC reshen jihar Ribas, wadda ta bayyana matakin tsigewar a matsayin wanda zai ƙara hargitsa jihar.

Rahotanni sun nuna cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kira wani taron sirri a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja, inda ya gana da Fubara da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, wanda shi ne tsohon gwamnan Ribas kuma uban siyasar Fubara.

Wike ya tabbatar da ganawar, yana mai cewa Shugaban ƙasa ne ya jagoranci sulhun domin kawo ƙarshen rikicin siyasar jihar. Ya bayyana fatansa cewa wannan karo zai zama na ƙarshe da aka shiga tsakani.

Wannan shi ne karo na biyu da ake ƙoƙarin tsige Fubara da mataimakiyarsa, bayan irin wannan yunƙuri a watan Maris 2025 ya haddasa babbar rikicin kundin tsarin mulki. A wancan lokaci, Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar, ya dakatar da gwamna, mataimakiyarsa da ‘yan majalisa na tsawon watanni shida, tare da naɗa Ibokette Ibas a matsayin mai kula da jihar na wucin gadi.

Daga bisani, an sasanta rikicin ta hanyar sulhu tsakanin Fubara, Wike da ‘yan majalisa, wanda ya ba gwamnan damar komawa kan kujerarsa.

Yanzu haka, dakatar da tsigewar na nuni da cewa ana neman mafita ta siyasa da shari’a domin kauce wa sake faɗawa cikin wani sabon rikici a jihar.

By ukarofi